1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ بُسْرٍ رَضِيَ اللَّهِ عَنْهُ قَالَ: أَتَى النَّبِيَّ رَجُلٌ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ! إِنَّ شَرَائِعَ الإِسْلَامِ قَدْ كَثُرَتْ عَلَيْنَا، فَبَابٌ نَتَمَسَّكُ بِهِ جَامِعٌ؟ قَالَ:
«لاَ يَزَالُ لِسَانُكَ رَطْبًا مِنْ ذِكْرِ اللَّهِ». وفي رواية: مِنْ حَدِيثِ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: آخِرُ مَا فَارَقْتُ عَلَيْهِ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ قُلْتُ: أَيُّ الأَعْمَالِ خَيْرٌ وَأَقْرَبُ إِلَى اللَّهِ؟ قَالَ: «أَنْ تَمُوتَ وَلِسَانُكَ رَطْبٌ مِنْ ذِكْرِ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ».

Daga Abdullahi ibnu Busr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum Ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah! Lallai cewa shari'un Musulunci sun yawaita a kanmu, to wace ƙofa ce mai tattarowa zamu yi riƙo da ita? ya ce:
«Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah». A cikin wata riwayar: Daga hadisin Mu'azu ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi -: Ƙarshen abin da na rabu da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kansa shi ne na ce: Wane aiki ne daga cikin ayyuka ya fi kuma ya fi kusanci zuwa ga Allah? Ya ce: «Ka mutu alhali harshenka yana ɗanye daga ambatan Allah».

Ingantacce ne Ahmad ne ya ruwaito shi da Tirmizi da Ibnu Majah da kuma Ibnu Hibban Arba’una Annawawi - 50

Bayani

Wani mutum ya kai ƙara wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa nafilifilin ibadu sun yi masa yawa har ya gajiya daga yin su saboda rauninsa, sannan ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi ga wani aiki mai sauki mai jawo lada mai yawa wanda zai rataya da shi ya yi riƙo da shi.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nunar masa harshensa ya zama ɗanye mai motsawa saboda dawwamar ambatan Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - a kowane lokaci da hali; na tasbihi da tahmidi da istigafari da addu'a da makamancin hakan.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar dawwama akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Daga girman falalar Allah (akwai) sawwaƙe sabubban lada.
  3. Fifikon bayi a rabonsu na ƙofofin aikin lada da alheri.
  4. Yawan ambatan Allah da harshe tasbihi da tahmidi da hailala da kabbara da wanin hakan, tare da dacewar zuciya yana tsayawa matsayin yawa da yawan nafilifilin ayyukan ɗa'a.
  5. Lurarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga masu tambaya da amsawa kowa da abinda ya dace da shi.

Manufofin Fassarorin

56 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو