1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba

عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«كل مُسْكِرٍ خَمْرٌ، وكل مُسْكِرٍ حرام، ومن شرِب الخمر في الدنيا فمات وهو يُدْمِنُهَا لَمْ يَتُبْ، لَمْ يَشْرَبْهَا في الآخرة».

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba".

Ingantacce ne Muslim ne ya ruwaito shi, shi kuwa Bukhari ya ruwaito jimla ta karshe ne ta Hadisin Sahih Muslim - 2003

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abinda yake kawar da hankali kuma ya tafiyar da shi to shi giya ne mai sa maye daidai ne ya kasance sha ne ko ci ko shaƙa ko makamancin hakan, kuma dukkan abinda yake sa maye kuma ya kawar da hankali to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta shi kuma Ya yi hani daga gare shi, ƙanƙaninsa da mai yawansa. Kuma dukkan wanda ya sha kowanne nau'i daga Nau’ukan waɗannan masu sa mayen, kuma ya lazimci shansu bai tuba ba daga gare su har ya mutu; to shi ya cancanci uƙubar Allah ta hanyar haramta masa shan ta a aljanna.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Illar haramta giya shi ne maye, dukkan abinda yake sa maye daga kowanne nau'i ya kasance to haramun ne.
  2. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
  3. Shan giya a cikin aljanna yana daga cikar jin daɗi da cikar ni'ima.
  4. Wanda bai kame kansa daga shan giya a duniya ba Allah Zai haramta masa shan ta a cikin aljanna. Sakamako yana zuwa ne daga jinsin aiki.
  5. Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba daga zunubai kafin mutuwa.

Manufofin Fassarorin

61 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو