1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya

عن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه:
أنه كَانَ يُكَبِّرُ فِي كُلِّ صَلَاةٍ مِنَ الْمَكْتُوبَةِ وَغَيْرِهَا، فِي رَمَضَانَ وَغَيْرِهِ، فَيُكَبِّرُ حِينَ يَقُومُ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْكَعُ، ثُمَّ يَقُولُ: سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، ثُمَّ يَقُولُ: رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ، قَبْلَ أَنْ يَسْجُدَ، ثُمَّ يَقُولُ: اللهُ أَكْبَرُ حِينَ يَهْوِي سَاجِدًا، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْفَعُ رَأْسَهُ مِنَ السُّجُودِ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَسْجُدُ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْفَعُ رَأْسَهُ مِنَ السُّجُودِ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَقُومُ مِنَ الْجُلُوسِ فِي الِاثْنَتَيْنِ، وَيَفْعَلُ ذَلِكَ فِي كُلِّ رَكْعَةٍ، حَتَّى يَفْرُغَ مِنَ الصَّلَاةِ، ثُمَّ يَقُولُ حِينَ يَنْصَرِفُ: وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، إِنِّي لَأَقْرَبُكُمْ شَبَهًا بِصَلَاةِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِنْ كَانَتْ هَذِهِ لَصَلَاتَهُ حَتَّى فَارَقَ الدُّنْيَا.

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -
Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa kafin ya yi sujjada, sannan ya ce: Allah ne mafi girma a yayin da yake tafiya ƙasa don yin sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa daga zama a raka'a ta biyu, zai aikata haka a kowacce raka'a, har sai ya gama sallar, sannan ya ce a yayin da yake juyawa: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 803

Bayani

Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana ruwaito wani yanki daga siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, yana ba da labarin cewa ya kasance idan ya tashi yin sallah yana kabbarar harama a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake cirata zuwa ruku'u, da yayin da yake yin sujjada, da yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, da yayin da yake yin sujjada ta biyu, da yayin da yake ɗago kansa daga gareta, da yayin da yake miƙewa daga raka'a biyun farko bayan zama don tahiyar farko a sallah mai raka'a uku ko huɗu, sannan ya aikata hakan a dukkanin sallah har sai ya gamata, ya kasance yana cewa a yayin da ya ɗago bayansa daga ruku'u: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce alhalin yana tsaye: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata a gareKa.
Sannan Abu Huraira yake cewa a yayin da ya idar da sallar: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai ni ne mafi kusancinku kamaceceniya da sallar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce siffar sallarsa har ya bar duniya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kabbara tana kasancewa a yayin kowanne sunkuyawa da ɗagowa, sai dai a ɗagowarsa daga ruku'u yana cewa: Allah Ya jin wanda ya gode maSa.
  2. Kwaɗayin sahabbai a kan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kiyaye sunnarsa.

Manufofin Fassarorin

61 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية