1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Sabuntawa Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عنه سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ:
«قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: {الْحَمْدُ لِلهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}، قَالَ: مَجَّدَنِي عَبْدِي، -وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي-، فَإِذَا قَالَ: {إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ}، قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ: {اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ، صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلا الضَّالِّينَ}، قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan bawa ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: bawaNa ya godemin, idan ya ce: {Mai kyauta a duniya mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: BawaNa ya yabeni, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakayya}, Zai ce: BawaNa ya girmamaNi, - wani lokaci kuma ya ce: bawaNa ya fawwala (al'amuransa) gareNi -, idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka kaɗai muke neman taimako}, sai Ya ce: Wannan tsakanina da tsakanin bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan ya ce: {ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar waɗanda Ka yi ni'ima a garesu ba waɗanda Ka yi fushi a kansu ba, ba kuma ɓatattu ba}, zai ce: Wannan ga bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 395

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa a hadisi Qudsi: Na raba Surar fatiha a sallah gida biyu tsakanina da tsakanin bawaNa, rabinta nawa ne, rabinta kuma nasane.
Rabinta na farko: Godiya ne da yabo da girmama Allah, zan saka masa da mafificin sakamako.
Rabinta na biyu: Ƙanƙar da kai ne da addu'a, zan amsa masa, kuma zan ba shi abin da ya roƙa.
Idan mai sallah ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah zai ce: BawaNa ya gode min, idan ya ce; {Mai kyauta a duniya Mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah zai ce: BawaNa ya yabeni, sai ya yabeNi ya yi iƙirari da gamewar baiwa ga halittata, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakamako}, Allah zai ce: BawaNa ya girmamaNi, ita ce ɗaukaka mayalwaciya.
Idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka ne kaɗai muke neman taimako}, Allah zai ce: Wannan tsakanina ne da tsakanin bawaNa.
Ɓangare na farko daga wannan ayar shi ne: {Kai kaɗai muke bautawa} shi ne iƙirari da Allantakar Allah, da kuma amsawa ga yin bauta, da shi ne ɓangaren da yake ga Allah ya kare.
Ɓangare na biyu daga ayar shi ga bawa ne: {Gareka ne kaɗai muke neman taimako} neman taimako daga Allah ne, da kuma alƙawarinSa na taimako.
Idan ya ce: {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya* Hanyar waɗanda Ka yi ni'ima garesu, ba waɗanda Ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba}, Allah zai ce: Wannan ƙanƙar da kai ne da addu'a daga bawaNa, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, haƙiƙa na amsa addu'arsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girman sha'anin Fatiha haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - ya ambaceta (Sallah).
  2. Bayanin kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bawanSa, yayin da ya gode maSa sabo da godewarSa da yabonSa da girmamaShi, kuma Ya yi masa alƙawari zai ba shi abin da ya roƙa.
  3. Wannan surar mai girma ta ƙunshi godiya ga Allah, da ambaton makoma, da roƙon Allah, da tsarkake ibada gareShi, da roƙon shiriya zuwa hanya madaidaiciya, da gargaɗi a kan hanyoyin ƙarya ( bata ) .
  4. Jin wannan hadisin (ji irin na halarto da ma'anarsa) ga mai sallah - idan ya karanta fatiha - zai ƙara masa khushu'insa a sallarsa.

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية