1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Mune ƙarshen al'ummu, kuma waɗanda za'a fara yi wa hisabi

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«نَحْنُ آخِرُ الأُمَمِ، وَأَوَّلُ مَنْ يُحَاسَبُ، يُقَالُ: أَيْنَ الأُمَّةُ الأُمِّيَّةُ وَنَبِيُّهَا؟ فَنَحْنُ الآخِرُونَ الأَوَّلُونَ».

Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Mune ƙarshen al'ummu, kuma waɗanda za'a fara yi wa hisabi, za’a ce: Ina al'ummar nan ba'uwa da kuma Annabinta? mune na ƙarshe kuma na farko».

Ingantacce ne Ibnu Majah ne ya ruwaito shi Sunanu Ibn Majah - 4290

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa al'ummarsa ita ce ƙarshen al'ummu a samuwa da kuma zamani, kuma ita ce farkon al'ummu da za’a yi wa hisabi a ranar alƙiyama, a ranar alƙiyama za'a ce: Ina al'ummar nan (ummiyya) ba'uwa da Annabinta? An dangantata ne zuwa ummiyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin rashin iya karatu da kuma rubutu. Za'a kirasu dan yin hisabi a farko, dan haka mune na ƙarshe a zamani da kuma samuwa, kuma na farko a hisabi da kuma shiga aljanna a ranar alƙiyama.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Fifikon wannan al'ummar akan sauran al'ummu da suka gabata.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية