1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya zo musu alhali su suna masu rinjaye

عَنِ المُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ يَزَالُ طَائِفَةٌ مِنْ أُمَّتِي ظَاهِرِينَ، حَتَّى يَأْتِيَهُمْ أَمْرُ اللَّهِ وَهُمْ ظَاهِرُونَ».

Daga Mugira Ɗan Shu'uba - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya zo musu alhali su suna masu rinjaye».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 7311

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu mutane ba za su taɓa gushewa ba daga al'ummata suna masu rinjaye akan mutane, masu rinjayar waɗanda suka saɓa musu, hakan har sai al'amarin Allah ya zo musu ta hanyar karɓar rayukansu a ƙarshen zamanin duniya kafin tashin alƙiyama.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mu'ujiza bayyananniya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa wannan siffar bata gushe ba da godiyar Allah tun daga zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har zuwa yanzu, kuma (wannan siffar) ba za ta gushe ba har sai al'amarin Allah ya zo wanda aka ambata a cikin hadisin.
  2. Falalar tabbata akan gaskiya da kuma aiki da ita, da kwaɗaitarwa akan hakan.
  3. Rinjayar Addini nau'i biyu ne: Kodai rinjaye da hujja da kuma bayani da bayyana, ko rinjaye da ƙarfi da kuma makami, kuma rinjayen mai wanzuwa ne da hujja da kuma bayani; domin cewa hujjar Musulunci ita ce Alƙur'ani, shi mai rinjaye ne kuma mai nasara ne akan maƙiyansa, sai dai nau'i na biyu na rinjaye, shi ne rinjayen ƙarfi da makami to wannan da gwargwadan imani ne da kuma tabbata a cikin ƙasa.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية