1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini)

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا قَالَ:
مَا قَاتَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَوْمًا قَطُّ حَتَّى يَدْعُوَهُمْ.

Daga Abdullahi Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini).

Ingantacce ne Ahmad da Baihaki suka Rawaito shi Sunan Al-Baihaki - 18232

Bayani

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa farawa da yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu zuwa ga Musulunci a farko, idan ba su amsa kiransa ba sai ya yaƙe su.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An sharɗanta kira zuwa ga Musulunci kafin yaƙi idan Musuluncin bai isa zuwa garesu ba.
  2. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana kiransu zuwa Musulunci, idan sun ƙi sai ya bijiro musu da bada da jizya, idan sun ƙi sai ya yaƙesu, kamar yadda ya zo a cikin wasu hadisan daban.
  3. Hikima a cikin yaƙi ita ce shigar mutane cikin Addinin Musulunci, ba wai kwaɗayi a kan bayinsu ko dukiyoyinsu da garuruwansu ba.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية