1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيَّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ -وَكَانَ غَزَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ثِنْتَيْ عَشْرَةَ غَزْوَةً- قَالَ: سَمِعْتُ أَرْبَعًا مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَعْجَبْنَنِي، قَالَ:
«لاَ تُسَافِرِ المَرْأَةُ مَسِيرَةَ يَوْمَيْنِ إِلَّا وَمَعَهَا زَوْجُهَا أَوْ ذُو مَحْرَمٍ، وَلاَ صَوْمَ فِي يَوْمَيْنِ: الفِطْرِ وَالأَضْحَى، وَلاَ صَلاَةَ بَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ، وَلاَ بَعْدَ العَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ، وَلاَ تُشَدُّ الرِّحَالُ إِلَّا إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: مَسْجِدِ الحَرَامِ، وَمَسْجِدِ الأَقْصَى، وَمَسْجِدِي هَذَا».

Daga Abu sa'id AlKhudr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance ya yi yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yaƙi goma sha biyu - ya ce: Na ji abubuwa hudu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka ƙayatar dani, ya ce:
"Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta, Babu azumi a ranaku biyu: Karamar sallah da babbar sallah, kuma babu sallah bayan asuba har sai rana ta bullo, kuma babu bayan la'asar har sai ta fadi, kuma ba'a daure sirdi (nikar gari domin tafiya) sai a masallatai uku: Masallaci mai alfarma, da masallacin Kudus, da masallacina wannan".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1995

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana abubuwa hudu:
Na farkonsu: Hana mace daga tafiyar kwana biyu ba tare da mijinta ba ko daya daga muharramanta ba, shi ne wanda ta haramta agare shi haramci na har'bada daga 'yan uwa, kamar Da, da uba, da Dan dan uwa da dan 'yar uwa, da baffa da kawu, da makamancin hakan.
Na biyunsu: Hani daga azimin ranar ƙaramar sallah da ranar babbar sallah, duk daya ne musulmi ya azimce su ne akan bakance (alwashi) ko nafila, ko kuma kaffara.
Na ukunsu: Hani daga sallar nafila bayan sallar la'asar har sai rana ta fadi, da bayan bullowar alfijir har sai rana ta bullo.
Na hudunsu: Hani daga tafiya zuwa wani wuri daga wurare da ƙudirce falalarsu da ƙudirce ninkin kyawawan lada a cikinsu, in banda wadannan masallatan uku, to ba'a daure sirdi ga wasunsu dan yin sallah a cikinsu, domin lada ba'a ninkashi sai a wadannan masallatan uku: Masallaci mai alfarma (Dake Makka), da masallacin Annabi (Dake Madina), da masallacin Kudus (Dake Falasdin).

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rashin halaccin tafiyar mace ba tare da muharrami ba.
  2. Mace ba muharrama ba ce ga mace a tafiya; Saboda fadinsa: "Mijinta ko muharraminta".
  3. Dukkan abinda ake kira tafiya to mace an hanata ta yi ba tare da miji ko muharrami ba, wannan hadisin ya kasance ne gwargwadan halin mai tambaya da wurinsa.
  4. Muharamin mace shi ne mijinta ko wanda ya haramta ta aure shi har abada, saboda kusanci kamar uba da Da da baffa da kawu. Ko shayarwa kamar uba na shayarwa da baffa na shayarwa, ko surukuta kamar baban miji, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce, domin abin nufi daga muaharrami kare mace da tsareta da tsayuwa da sha'aninta.
  5. Kulawar shari'ar Musulunci da mace, da kareta da tsareta.
  6. Rashin ingancin sallar nafila kowacce bayan sallar Asuba da la'asar, an toge daga hakan rama farillan da suka wuce, da masu sabubba, kamar gaisuwar masallaci da makamancin hakan.
  7. Sallah ta haramta bayan bullowar rana kai tsaye, domin babu makawa sai ta dago gwargwadan goron mashi, da abinda ya yi kusa na mintina goma zuwa sha biyar a kusance.
  8. Lokacin la'asar yana mikewa zuwa faduwar rana.
  9. A cikinsa akwai halaccin daure sirdi (domin tafiya) zuwa masallatai uku.
  10. Falalar masallatai uku da fifikonsu akan wasunsu.
  11. Rashin halaccin tafiya dan ziyartar ƙaburbura koda ya kasance ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ne, amma ziyararsa ta halatta ga wanda yake a Madina, ko ya zo Madina dan wata buƙatar da aka shara'anta ko aka halatta.

Manufofin Fassarorin

57 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية