1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ يُصَلِّي أَحَدُكُمْ فِي الثَّوْبِ الوَاحِدِ لَيْسَ عَلَى عَاتِقَيْهِ شَيْءٌ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 359

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi sallah a tufa ɗaya ya tsiraitar da kafaɗunsa abinda ke tsakanin kafaɗa da wuya ta inda kada, ya sarayar da wani abinda zai suturtasu; domin kafaɗu biyu duk da ba al'aura ba ne, to lallai suturtasu ya fi tabbata a ɓoye al'aura, kuma shi ne mafi kusanci zuwa girmama Allah - Maɗaukakin sarki - da girmamaShi a tsakiyar tsayuwa a gabanSa a cikin sallah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin sallah a tufa ɗaya idan ya suturta abinda suturta shi yake zama wajibi.
  2. Halaccin sallah a tufa biyu, ɗayansu zai suturta saman jiki, ɗayan kuma zai suturta ƙasansa.
  3. An so kasancewar mai sallah (ya kasance) a kyakkyawar siffa.
  4. Wajabcin suturce kafaɗu biyu ko ɗayansu a cikin sallah, idan hakan ya tabbata gare shi , an ce hanin na tsarkaka ne (bana haramci ba ne).
  5. Karancin abinda ke a hannun sahabbai - Allah Ya yarda da su - na dukiya, har sashinsu ba ya mallakar tufa biyu.
  6. AlNawawi ya ce a ma'anar hadisin: Hikimarsa cewa shi idan ya ɗaura shi alhali bai kasance akwai wani abu akan kafaɗarsa ba ba'a amintuwa cewa al'aurarsa ta yaye, saɓanin idan ya sanya sashinsa akan kafaɗarsa, kuma domin shi zai iya buƙatuwa zuwa ya kamo shi da hannunsa ko da hannayensa sai ya shagalta da hakan, sai sunnar ɗora hannun dama akan na hagu ƙarƙashin ƙirji da kuma ɗaga su inda aka shara'anta ɗaga su dama wanin hakan su wuce shi; domin a cikinsa akwai barin suturce saman jiki da wurin ado, alhali haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ku riƙi adonku a kowane masallaci} [al-Aaraf: 31].

Manufofin Fassarorin

48 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية