1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a kasuwa, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana yin afuwa kuma yana kau da kai

عَن أَبي عَبْدِ اللهِ الْجَدَلِيِّ قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها عَنْ خُلُقِ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم فَقَالَتْ:
لَمْ يَكُنْ فَاحِشًا وَلَا مُتَفَحِّشًا وَلَا صَخَّابًا فِي الْأَسْوَاقِ، وَلَا يَجْزِي بِالسَّيِّئَةِ السَّيِّئَةَ وَلَكِنْ يَعْفُو وَيَصْفَحُ.

Daga Abu Abdullahi al-Jadali ya ce: Na tambayi A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce:
Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a kasuwa, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana yin afuwa kuma yana kau da kai.

Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 2016

Bayani

An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Alfasha da munanan maganganu ko ayyuka ba su zama daga ɗabi'unsa ba, kuma ba ya ɗorawa kansa alfasha, kuma ba ya yi da gangan, kuma ba ya ihu yana ɗaga muryarsa a cikin kasuwanni, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana sakayya da kyakkyawa, kuma yana yin afuwa a baɗini, kuma yana kau da kai yana kawar dakai a zahiri.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yake a kansa na manyan ɗabi'u, da nisanta daga ɗabi'u ababen zargi.
  2. Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan ɗabi'u da kuma nisantar munanan ɗabi'u.
  3. Zargin yin magana da munananawa a magana da kuma mummunan zance.
  4. Zargin ɗaga murya ga mutane dayi musu ihu.
  5. Kwaɗaitarwa akan rama mummuna da kyakkyawan abu da kuma yin afuwa da kau da kai.

Manufofin Fassarorin

42 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية