1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah

عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه قَالَ:
سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الرَّجُلِ يُقَاتِلُ شَجَاعَةً، وَيُقَاتِلُ حَمِيَّةً، وَيُقَاتِلُ رِيَاءً، أَيُّ ذَلِكَ فِي سَبِيلِ اللهِ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ قَاتَلَ لِتَكُونَ كَلِمَةُ اللهِ هِيَ الْعُلْيَا، فَهُوَ فِي سَبِيلِ اللهِ».

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 1904

Bayani

An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga saɓanin manufofin masu yin yaƙi; wanda ya yi yaƙi dan jarumtaka ko ƙabilanci ko dan aga matsayinsa a cikin mutane ko wanin hakan, wannene saboda Allah? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya yi yaƙi saboda Allah shi ne: Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Asali a cikin gyaruwar ayyuka da ɓacinsu (ita ce) niyya da tsarkake aiki saboda Allah.
  2. Idan manufa daga yaƙi ita ce ɗaukaka kalmar Allah, kuma wata manufar daban abar shara'antawa ta haɗu a cikinsa, kamar samun ganima, to shi ba ya cutarwa.
  3. Kare maƙiya daga shiga garuruwa da mutuncin mata yana daga yaƙi saboda Allah.
  4. Falalar da ta zo a cikin mayaƙa tana keɓantuwa ne ga wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah - Maɗaukakin sarki - ta zama ita ce maɗaukakiya.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية