1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa ‌Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta

عنْ ابنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
كُنَّا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَانْطَلَقَ لِحَاجَتِهِ، فَرَأَيْنَا حُمَّرَةً مَعَهَا فَرْخَانِ، فَأَخَذْنَا فَرْخَيْهَا، فَجَاءَتِ الْحُمَرَةُ فَجَعَلَتْ تَفْرِشُ، فَجَاءَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «مَنْ فَجَعَ هَذِهِ بِوَلَدِهَا؟ رُدُّوا وَلَدَهَا إِلَيْهَا»، وَرَأَى قَرْيَةَ نَمْلٍ قَدْ حَرَّقْنَاهَا، فَقَالَ: «مَنْ حَرَّقَ هَذِهِ؟» قُلْنَا: نَحْنُ. قَالَ: «إِنَّهُ لَا يَنْبَغِي أَنْ يُعَذِّبَ بِالنَّارِ إِلَّا رَبُّ النَّارِ».

Daga Ibu Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce:
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin tafiya, sai ya tafi wata buƙatarsa, sai muka ga wata tsuntsuwa tare da 'yayanta biyu, sai muka ɗauke su, sai tsuntsuwar ta zo tana fakan-fakan (tana nemansu), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Waye ya raba wannan da ɗanta? ku maida mata da ɗanta», kuma sai ya ga wasu ramin tururuwa wanda muka ƙona shi, sai ya ce: «‌Waye ya ƙona wannan?» mukace: Mune. Ya ce: «‌Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta».

Ingantacce ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi Sunan Abi Dawud - 2675

Bayani

Abdullahi Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tafi dan wata buƙatarsa, sai sahabbansa suka samu wata tsuntsuwa tare da 'ya'yanta biyu, sai suka ɗaukesu, sai tsuntsuwar ta fara fakan-fakan da fukafukanta tana buɗesu dan firgicin rasa 'ya'yanta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma ya ce: Waye ya baƙanta mata rai ya tsoratar da ita ta hanyar ɗauke mata 'ya'yanta?! Sannan ya yi umarni a mayar mata da su. Sannan ya ga wani ramin tururuwar da aka ƙona shi da wuta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Waye ya ƙona wannan? Wasu daga cikin sahabbansa suka ce: Mu ne. Sai ya ce da su: Lallai ba ya halatta ga wani ya azabtar da mai rai da wuta; sai Allah Mahaliccinta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin ɓoyuwa don biyan buƙata (kewayawa).
  2. Hani daga azabtar da dabbobi ta hanyar ɗaukar 'ya'yansu.
  3. Hani daga ƙona tururuwa da ƙwari da wuta.
  4. Kwaɗaitarwa akan rangwami da tausayawa dabbobi, kuma Musulunci ya rigaya da hakan.
  5. Jinƙansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga dabbobi.
  6. Azabtarwa da wuta yana daga abinda Ubangiji - Mai girma da ɗaukaka - Ya keɓanta da shi.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية