1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna

عَن الحَسَنِ قال: حَدَّثنا جُنْدَبُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، فِي هَذَا المَسْجِدِ، وَمَا نَسِينَا مُنْذُ حَدَّثَنَا، وَمَا نَخْشَى أَنْ يَكُونَ جُنْدُبٌ كَذَبَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلّى الله عليه وسلم:
«كَانَ فِيمَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ رَجُلٌ بِهِ جُرْحٌ، فَجَزِعَ، فَأَخَذَ سِكِّينًا فَحَزَّ بِهَا يَدَهُ، فَمَا رَقَأَ الدَّمُ حَتَّى مَاتَ، قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: بَادَرَنِي عَبْدِي بِنَفْسِهِ، حَرَّمْتُ عَلَيْهِ الجَنَّةَ».

Daga Hassan ya ce: Jundub ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi mana hadisi a cikin wannan masallacin, kuma bamu manta ba tun da ya yi mana hadisin, kuma bama jin tsoron cewa Jundub ya yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 3463

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninku ya kasance rauni ya same shi, sai ya kasa haƙuri bai yi haƙuri akan raɗaɗin ba, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa da ita kuma ya gaggautowa mutuwa, jinin bai tsaya ba har ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawa Na ya yi miNi gaggawa da ransa, haƙiƙa na haramta masa aljanna.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar haƙuri akan jarrabawa, da barin ƙorafi saboda raɗaɗi dan kar ya kai zuwa mafi tsanani daga gare shi.
  2. Bayar da bayanin al'ummun da suka shuɗe da abinda a cikinsa akwai alheri da kuma wa'azi.
  3. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai tsayuwa a wurin haƙƙoƙin Allah da kuma rahamarSa ga halittarSa inda Ya haramta musu kashe rayukansu, kuma cewa rayuka mallakin Allah ne.
  4. Haramta aikata sabubban da zasu kai zuwa kashe rai, da kuma narko mai tsanani a cikin hakan.
  5. Ibnu Hajar ya ce: Hakan ya yi nuni akan ya yanke hannun ne dan nufin mutuwa ba dan nufin yin maganin da yake kyakkyawan zai yi anfani da shi ba.

Manufofin Fassarorin

44 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية