1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa ‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضيَ اللهُ عنهما:
أنَّهُ قَالَ لعَطَاءِ بْنِ أَبِي رَبَاحٍ: أَلَا أُرِيكَ امْرَأَةً مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَ: هَذِهِ الْمَرْأَةُ السَّوْدَاءُ، أَتَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: إِنِّي أُصْرَعُ وَإِنِّي أَتَكَشَّفُ، فَادْعُ اللهَ لِي، قَالَ: «إِنْ شِئْتِ صَبَرْتِ وَلَكِ الْجَنَّةُ، وَإِنْ شِئْتِ دَعَوْتُ اللهَ أَنْ يُعَافِيَكِ» قَالَتْ: أَصْبِرُ، قَالَتْ: فَإِنِّي أَتَكَشَّفُ فَادْعُ اللهَ أَنْ لَا أَتَكَشَّفَ، فَدَعَا لَهَا.

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su:
Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 2576

Bayani

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah: Shin bana nuna maka wata mata daga cikin 'yan aljanna ba? Aɗa'u ya ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar mutuniyar Habasha, ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Lallai cewa ni ina da cutar farfaɗiya kuma cewa ni ina yin tsirara wani abu yana yayewa daga jikina alhali ni ban sani ba, to ka roƙamin Allah Ya yaye mini, ya ce: Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki, ta ce: To zan yi haƙurin, sannan ta ce: To ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara idan na yi farfaɗiya, sai ya roƙa mata Allah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haƙuri akan bala'i a duniya yana gadar da aljanna.
  2. Nawawi ya ce: A cikin sa akwai dalili akan cewa farfaɗiya ana bada lada a kanta mafi cikar lada.
  3. Kamewa da kunyar matan sahabbai, da kuma kwaɗayinsu akan suturta - Allah Ya yarda da su -, wannan matar ta kasance mafi yawan abinda take jin tsoro shi ne wani abu ya yaye daga jikinta.
  4. Ibnu Hajar ya ce: Lallai yin riƙo da tsanani shi yafi daga yin riƙo da rangwami ga wanda ya san cewa akan kansa zai iya, kuma ba zai yi rauni ba saboda lazimtar tsanani.
  5. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa cewa maganin cututtuka gaba ɗayansu shi ne addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah ya fi tasiri kuma ya fi amfani daga magani da ƙwayoyi, kuma cewa tasirin hakan da kuma tasirin jiki daga gare shi ya fi girma daga tasirin magungunan jiki, sai dai kaɗai yana tasiri ne da al'amura biyu: Na farkonsu ta ɓangaren wanda illar ta sama shi ne gaskiyar nufi, ɗayan kuma ta ɓangaren mai yin maganin, shi ne ƙarfin niyya da kuma ƙarfin zuciyarsa da tsoron Allah da kuma dogara, Allah ne Mafi sani.
  6. Ibnu Hajar ya ce; A cikinsa akwai dalili akan halaccin barin yin magani.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية