1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا يَزَالُ البَلاَءُ بِالمُؤْمِنِ وَالمُؤْمِنَةِ فِي نَفْسِهِ وَوَلَدِهِ وَمَالِهِ حَتَّى يَلْقَى اللَّهَ وَمَا عَلَيْهِ خَطِيئَةٌ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".

Hasan ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 2399

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa bala'i da jarraba ba zasu gushe ba ga bawa mumini da mumina, a kansa da lafiyarsa da jikinsa, da 'ya'yansa na rashin lafiya ko mutuwa ko sabawa ko wanin haka, haka a dukiyarsa na bukatuwa da tafiya kasuwanci da sata, da tawayar rayuwa da kunci a cikin arziki, har Allah Ya kankare masa dukkanin zunubansa da kurarkuransa da wannan bala'in har idan ya gamu da Allah zai zama ya tsarkaka daga dukkan zunubai da kurakuran da ya aikata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Daga cikin rahamar Allah ga bayinSa muminai shi ne ya kankare musu zunubansu a duniyarsu ta hanyar wasu masibu na duniya da aibobinta.
  2. Bala'i shi akarankansa yana kankare zunubai da sharaɗin imani, idan bawa ya yi hakuri bai yi fushi ba za'a ba shi lada.
  3. Kwaɗaitarwa akan hakuri a dukkan al'amura, cikin abinda yake so da abinda yake ki, ya yi hakuri har ya bada abinda Allah Ya wajabta masa, kuma ya yi hakuri har ya nisanci abinda Allah Ya haramta, yana kwaɗayin ladan Allah, kuma yana tsoron ukubarSa.
  4. FaɗinSa: "Da mumini da mumina", karin lafazin mumina a cikinsa akwai dalili akan karin karfafawa ga mace; in ba haka ba da ya ce: "Da mumini" da mace ta shiga cikinsa; domin hakan ba ya kebantar namiji, idan bala'i ya afkawa mace to haka itama an yi mata alkawari da kwatankwacin wannan sakamakon na kankare zunubai da kurakurai.
  5. Falalar da ta jerantu akan bala'i tana daga abinda zai sawwakawa bawa abinda yake gamuwa da shi na raɗaɗi akai akai.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية