1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا مِنْ نَبِيٍّ بَعَثَهُ اللهُ فِي أُمَّةٍ قَبْلِي إِلَّا كَانَ لَهُ مِنْ أُمَّتِهِ حَوَارِيُّونَ، وَأَصْحَابٌ يَأْخُذُونَ بِسُنَّتِهِ وَيَقْتَدُونَ بِأَمْرِهِ، ثُمَّ إِنَّهَا تَخْلُفُ مِنْ بَعْدِهِمْ خُلُوفٌ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ، وَيَفْعَلُونَ مَا لَا يُؤْمَرُونَ، فَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِيَدِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِلِسَانِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِقَلْبِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَلَيْسَ وَرَاءَ ذَلِكَ مِنَ الْإِيمَانِ حَبَّةُ خَرْدَلٍ».

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi, sannan wasu masu sabawa zasu saba a bayansu suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umarce su ba, wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi muminin ne, kuma babu wani kwatankwacin kwayar komayya na imani bayan hakan".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 50

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan yakar masu sabawa shari'a da maganganunsu da kuma ayyukansu.
  2. Rashin yin inkari a zuciya dalili ne akan raunin imani ko tafiyarsa.
  3. Sawwakewar Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ga Annabwa ga wanda zai dauki sakonsu a bayansu.
  4. Wanda yake son tsira to ya wajaba ya bi tafarkin Annabawa; domin duk wata hanyar da ba hanyarsu ba to halaka ce kuma bata ce.
  5. Duk lokacin da zamani ya nisanta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - sai mutane su bar sunnoni kuma su bi soye-soyen zukatansu, kuma su farar da bidi'o'i.
  6. Bayanin matakan jihadi, cewa shi da hannu ne ga wanda zai iya canzawa, kamar shuwagabanni da mahukunta da sarakai, haka kuma da magana yana kasancewa ne ta hanyar bayyana gaskiya da kira zuwa gareta, haka kuma da zuciya yana kasancewa ne ta hanyar yin inkarin abin ki da rashin sonsa ko yarda da shi.
  7. Wajabcin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية