1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ:
فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ.

Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1503

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai bayan (azimin) Ramadan, ita gwargwadan Sa'i ne (wanda) awonsa yakai mudun Nabiyyi huɗu. Mudun Nabiyyi: (Shi ne) cikin tafukan mutum madaidaici, na dabino ko alkama akan kowane musulmi; ɗa da bawa, namiji da mace, ƙarami da babba, hakan ga wanda a wajensa akwai abinda ya rage daga abin cin yininsa da darensa, (zai fitarwa) kansa da kuma wanda yake kula da su. Kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Zakkar fidda kai ta azimi tana wajaba a fitar wa yaro ita da babba, da ɗa da bawa, kuma ana yi wa waliyyin (yaro) da mamallakin (bawa) umarni da ita, kuma mutum yana fitarwa kansa da 'ya'yansa da wanda ciyarwarsu take wajaba akansa.
  2. Zakkar fidda kai ba ta wajaba daga ɗan tayi, saidai an so (a fitar masa).
  3. Bayanin abinda ake fitarwa a zakkar fidda kai, shi ne abincin mutane na al'ada.
  4. Wajabcin fidda ita kafin sallar idi, abinda ya fi ta kasance a safiyar idi, kuma fitar da ita yana halatta kafin idi da kwana ɗaya ko kwanaki biyu.

Manufofin Fassarorin

46 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية