1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta

عن أبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يَحِلُّ لِامْرَأَةٍ مُسْلِمَةٍ تُسَافِرُ مَسِيرَةَ لَيْلَةٍ إِلَّا وَمَعَهَا رَجُلٌ ذُو حُرْمَةٍ مِنْهَا».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 1339

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana haramta akan mace musilma ta yi tafiyar dare (daya) sai idan akwai namji muharraminta tare da ita.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ibn Hajar ya ce: Rashin tafiya ga mace ba tare da muharrami ba, shi ijam'i ne a wanin Hajji da Umarh, da fita daga kasar shirka, daga cikinsu (malamai akwai) wanda ya sanya hakan daga sharuɗɗan Hajji.
  2. Cikar shari'ar musulunci, da kwaɗayinta akan kiyaye mace da kuma tsareta.
  3. Imani da Allah da ranar lahira suna lazimtar da ƙanƙar da kai ga shari'ar Allah, da kuma tsayuwa a iyakokinta.
  4. Muharramin mace shi ne mijinta ko wanda yake haramta a gareta (ta aure shi) har abada saboda 'yan uwantaka, ko shayarwa, ko sukurtaka, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce; domin cewa abin nufi daga muharrami (shi ne) tsare mace da kareta da tsayuwa da sha'aninta.
  5. AlBaihaƙi ya ce game da riwayoyin da suka zo a tsawon tafiyar da mace ba za ta yi tafiya ba sai tare da muharrami: Abin tabbatarwa cewa dukkan abinda ake ambatansa tafiya to an hana mace daga gare shi ba tare da miji ko muharrami ba, daidai ne ya kasance kwana uku ne ko kwana biyu ko kwana ɗaya ko tafiyar wasu awanni ko wanin haka; saboda riwayar Ibnu Abbas abar wawaitawa (Mutlaka ce), ita ce kuma ƙarshen riwayoyin Muslim wacce ta gabata: (Kada mace ta yi tafiya sai tare da muharraminta) wannan yana haɗa dukkan abinda ake ambatansa tafiya. Ya tiƙe. Wannan hadisin ya kasance gwargwadan mai tambaya ne da kuma ƙasarsa.

Manufofin Fassarorin

47 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية