1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa ‌Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضيَ اللهُ عنه:
أَنَّ جِبْرِيلَ أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ اشْتَكَيْتَ؟ فَقَالَ: «نَعَمْ» قَالَ: «بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ، مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ، اللهُ يَشْفِيكَ بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ».

Daga Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa (Mala’ika) Jibril ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Muhammad baka da lafiya ne? sai ya ce: «‌Eh» ya ce: «‌Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2186

Bayani

Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya tambaye shi: Ya Muhammad kana fama da rashin lafiya ne? Sai ya ce: Eh. Sai Mala’ika Jibril ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa ruƙya da faɗinsa: «‌Da sunan Allah» ina mai neman taimakonSa «‌Nake maka ruƙya» nake nema maka tsari. «‌Daga dukkan abinda yake cutar da kai» ƙarami ne ko babba. «‌Daga kowace rai» mummuna. «‌Ko maitar mai hassada» da ya kai gareka, Allah «‌Ya warkar da kai» kuma ya kareka daga dukkanin cutuka. «‌Da sunan Allah nake maka ruƙya» ya maimaita shi ne dan kai matuƙa, kuma ya fara da shi kuma ya rufe da shi dan nuni zuwa ga cewa babu wani mai amfanarwa sai Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin labarta rashin lafiya dan bayanin waƙi'in hali ba dan babin rashin haƙuri da kai kuka ba.
  2. Ruƙya tana halatta da sharuɗɗan nan masu zuwa: 1- Ta zama da Alƙur'ani ne ko da ambatan sunan Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma addu'o'in da aka shara'anta. 2- Ta zama da harshen larabci, ko da abinda ake sanin ma'anarsa daga wasu harsunan daban. 3- Ya ƙudirce cewa ruƙya ita akan kanta bata tasiri; kawai ita sababi ce daga cikin sabubban da basa tasiri sai da izinin Allah - Mai girma da ɗaukaka -. 4- Ta kaɗaita daga shirka, ko abinda aka haramta, ko bidi'a, ko abinda zai kai zuwa ga hakan.
  3. Tabbatar da cutar lambing baka ( ko maita), kuma cewa ita gaskiya ce, to yana kamata a nemi yin ruƙya daga gareta.
  4. An so yin ruƙya da abinda ya zo a cikin hadisi.
  5. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waninsa ne daga mutane, duk abinda yake samun waninsa na rashin lafiya zai iya samunsa.
  6. Kulawar Allah ga AnnabinSa- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kiyayeShi, da wakilta mala'ikunSa da hakan.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية