1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro

عَنْ عُثْمَانَ بْنِ أَبِي الْعَاصِ الثَّقَفِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ شَكَا إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَجَعًا يَجِدُهُ فِي جَسَدِهِ مُنْذُ أَسْلَمَ، فَقَالَ لَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«ضَعْ يَدَكَ عَلَى الَّذِي تَأَلَّمَ مِنْ جَسَدِكَ، وَقُلْ بِاسْمِ اللهِ ثَلَاثًا، وَقُلْ سَبْعَ مَرَّاتٍ أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ».

Daga Usman ɗan Abul Aas al-Saƙafi - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya kai kukan wani ciwo da yake jinsa a cikin jikinsa wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tunda ya musulunta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa:
"Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2202

Bayani

Wani ciwo ya kama Uman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya kusa ya halakar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo l ya duba shi, kuma ya sanar da shi wata addu'ar da Allah zai ɗauke masa abinda ya saukar masa na rashin lafiyar; shi ne ya ɗora hannunsa akan wurin da yake jin ciwon, kuma sai ya ce: Bismillah, (Da sunan Allah) sau uku, sannan ya ce sau bakwai: (Ina neman tsari) ina fakewa kuma ina katanguwa (Da Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji)na raɗaɗi a wannan lokacin (kuma nake tsoro) nake jin tsoron faruwarsa a nan gaba na baƙin ciki da tsoro, ko ya wannan cutar ta ci gaba kuma radadinta ya yadu a jiki.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so mutum ya yi wa kansa tawaida kamar ydda ya zo a cikin hadisin.
  2. Kai kuka - ba tare da kurari ba ko bijirewa - ba ya kore dogaro (ga Allah) da kuma haƙuri.
  3. Addu'a tana daga jumlar aikata sabubba, saboda haka yana kamata a takaitu da lafazzukanta da kuma adadinta.
  4. Wannan addu'ar tana kasancewa ne ga dukkan wani raɗaɗi na gaɓa.
  5. Ɗora hannu akan wurin raɗaɗi a lokacin yin tawaida da wannan addu'ar.

Manufofin Fassarorin

50 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية