1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne

عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«إنَّ الرُّقَى والتَمائِمَ والتِّوَلَةَ شِرْكٌ».

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa:
"Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".

Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad Sunan Abi Dawud - 3883

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana wasu abubuwa (waɗanda) aikatasu yana daga shirka; daga cikinsu akwai:
Na ɗaya: Tawaida: Zancen da 'yan Jahiliyya suke neman waraka da shi wanda ya haɗo shirka.
Na biyu: Layu na tsarkiya da makamancinta: Waɗanda ake ratayawa yara da dabbobi da wasunsu dan tunkuɗe kambun baka.
Na uku: Tiwala: Wacce akeyi don jawo soyayyar ɗaya daga cikin ma'aurata zuwa ɗayan.
Waɗannan al'amuran suna daga shirka; domin suna daga cikin riƙar abu a matsayin sababi, kuma shi ba sababi ne na shari'a ba wanda ya tabbata da dalili, ba kuma sababi ne na zahiri ba da ya tabbata da gwadawa. Amma sabubba na shari'a kamar karanta Al-ƙur'ani, ko na zahiri kamar magunguna da suka tabbata ta hanyar gwadawa, to, su sun halatta tare da ƙudire cewa su sabubba ne, kuma amfani da cuta suna hannun Allah ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kiyaye tauhidi da aƙida daga abin da yake ɓata su.
  2. Haramta yin amfani tawaida ta shirka da layu da tiwala.
  3. Ƙudirewar mutum a waɗannan abubuwa ukun cewa su sabubba ne: Shi ne shirka ƙarama; domin ya sanya abin da ba sababi ba ne a matsayin sababi, amma idan ya ƙudire cewa suna amfanarwa kuma suna cutarwa a kan kansu, to, shi shirka ne babba.
  4. Gargaɗi a kan aikata sabubba na shirka da kuma ababen haramtawa.
  5. Haramta (nau'o'in) tawaida kuma suna daga shirka, sai dai abin da aka shara'anta daga cikinsu.
  6. Ya kamata a rataya zuciya ga Allah Shi kaɗai, cuta da amfani daga gareshi ne Shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkuɗe sharri sai Allah - Maɗaukakin sarki -.
  7. Tawaida da ta halatta ita ce wacce ta tattaro sharuɗɗa uku; 1- Ya ƙudire cewa su sababi ne ba sa amfanarwa sai da izinin Allah. 2- Ta kasance da Al-ƙur'ani da kuma sunayen Allah da siffofinSa da addu'o'in Annabi da wasu ababen shara'antawa. 3- Ta zama da yare abin fahimta, kuma kada ta ƙunshi ɗalasimai (saƙandamai) da sha'awazah (surkulle).

Manufofin Fassarorin

68 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
EL Ελληνικά اليونانية
AK Akan الأكانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
RN Kirundi الكيروندي
YAO Yao الياو
KMR Kurmancî الكرمنجية