1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ka ce : Ya Allah Ka wadatar da ni da halalinKa daga barin haram ɗinKa, kuma Ka wadatani da falalarKa daga wanda ba Kai ba

عَنْ عَلِيٍّ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ مُكَاتَبًا جَاءَهُ، فَقَالَ: إِنِّي قَدْ عَجَزْتُ عَنْ مُكَاتَبَتِي فَأَعِنِّي، قَالَ: أَلاَ أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ عَلَّمَنِيهِنَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، لَوْ كَانَ عَلَيْكَ مِثْلُ جَبَلِ صِيرٍ دَيْنًا أَدَّاهُ اللَّهُ عَنْكَ، قَالَ:
«قُلْ: اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلاَلِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ».

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - cewa wani wanda aka ɗorawa fansa ya zo masa, sai ya ce: Haƙiƙa ni na kasa biyan fansa ta to ka taimakeni, ya ce: Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda mazon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da ni su, da a ce kana da bashi a kanka kwatankwacin dutsen Seer Allah Zai biya maka, ya ce:
"Ka ce : Ya Allah Ka wadatar da ni da halalinKa daga barin haram ɗinKa, kuma Ka wadatani da falalarKa daga wanda ba Kai ba".

Hasan ne Tirmizi ne ya ruwaito shi Sunan Tirmizi - 3563

Bayani

Wani bawa wanda mai shi ya ɗorawa fansa kuma ya yi ittifaƙi tare da shi akan ya sayi kansa ya 'yantata dan ya zama ɗa, kuma ba shi da dukiya, ya zo wurin sarkin muminai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: Haƙiƙa ni na gajiya (na kasa) daga biyan abinda ke kaina to ka taimakeni akan biyansa da dukiya, ko da koyarwa da shiryarwa, sai sarkin muminai ya ce masa; Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani su, da a ce a kanka akwai bashi kwatankwacin wani dutse mai suna Seer na ƙabilar Ɗayyu ne da Allah Ya biya maka shi zuwa ga mai shi, kuma Ya tsamoka daga ƙasƙancinsa, Ya ce: Ka ce: (Ya Allah Ka isar mini) Ka juyar mini Ka nisantar da ni (da halal ɗinKa) ina mai wadatuwa da ita, (daga) faɗawa a (haram ɗinKa), (Kuma Ka wadatar da ni) Ka isar mini (da falalarKa) samuwarKa (daga wanda ba Kai ba) cikin halitta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Neman shawara da neman ra'ayin ma'abota ilimi da Addini.
  2. Ya wajaba akan ma'abota ilimi da masu Da'awa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - nunawa waɗanda ake kira da shiryar dasu zuwa abinda zai taimakesu akan abinda yake bijiro musu na matsaloli.
  3. Kwaɗaitarwa akan taimakon wanda aka ɗorawa fansa.
  4. Kwaɗaitarwa akan neman sanin wannan addu'ar, da roƙon Allah da ita.
  5. Arziƙi na halal koda ya kadan ne shi ne mafi alheri daga dukiyar haram koda ta kasance mai yawa ce.
  6. Neman wadatuwa da Allah maimakon halittarsa.
  7. Kwaɗaitarwa akan amsawa mai tambaya amsawa mai kyau idan baka da abinda zaka ba shi.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية