1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah

عن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيَّ رَضِيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهُ صلَّى اللهُ عليهِ وَسَلَّم:
«لَقِّنُوا مَوْتَاكُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ».

Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah»

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 916

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa kan mu faɗi kuma mu maimaita kalamr Tauhidi "La'ilaha illallahu" a wurin wanda fizgar mutuwa ta zo masa har sai ya faɗeta, dan ta zama ƙarshen maganarsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so yi wa wanda mutuwa ta halarto masa talƙini.
  2. An karhanta yawaita yin talƙini ga wanda mutuwa ta halarto masa, da kuma nacewa a kansa idan ya karɓi talƙinin, ko an fahimci hakan daga gare shi; dan kada ya takura masa sai ya furta abin da bai dace ba.
  3. Nawawi ya ce: Idan ya faɗeta sau ɗaya to kada ya maimaita masa saidai idan ya yi wata maganar daban a bayansa, sai asake bijiro masa da ita dan ta zama ita ce ƙarshen zancensa.
  4. Hadisin ya ƙunshi halartar wurin da wanda mutuwa ta halarto masa dan tinatar da shi da kuma yi debe masa kewa da rintse idanuwansa da kuma tsayuwa da haƙƙoƙinsa.
  5. Rashin halaccin yin talƙini bayan mutuwa da wurin ƙabari bayan an binne; saboda rashin aikata hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية