1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لِبِلاَلٍ عِنْدَ صَلاَةِ الفَجْرِ:
«يَا بِلاَلُ، حَدِّثْنِي بِأَرْجَى عَمَلٍ عَمِلْتَهُ فِي الإِسْلاَمِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ دَفَّ نَعْلَيْكَ بَيْنَ يَدَيَّ فِي الجَنَّةِ» قَالَ: مَا عَمِلْتُ عَمَلًا أَرْجَى عِنْدِي أَنِّي لَمْ أَتَطَهَّرْ طَهُورًا، فِي سَاعَةِ لَيْلٍ أَوْ نَهَارٍ، إِلَّا صَلَّيْتُ بِذَلِكَ الطُّهُورِ مَا كُتِبَ لِي أَنْ أُصَلِّيَ.

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa Bilal yayin sallar Asuba:
"Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci, domin ni na ji takun takalmanka a gabana a cikin aljanna" Ya ce: Ban taɓa aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a gurina sai dai cewa bana yin wata alwala a lokacin dare ko rana, sai na sallaci abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1149

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin mafarki ya gan shi a cikin aljanna, sai ya cewa Bilal Ibnu Rabah: Bani labarin mafi kwaɗayin aikin nafilar da ka aikata shi a cikin Musulunci? Domin ni na ji ƙarar takalmanka a hankali lokacin da kake motsasu kana tafiya a gabana a cikin aljanna. Bilal ya ce: Ban aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a wurina sai dai cewa ni ban taɓa yin kari (hadasi) ba da daddare ko da rana ba face sa na yi alwala, sannan na yi sallah saboda Ubangijina, ta nafilfili kai tsaye abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar aikin da Bilal - Allah Ya yarda da shi - ya yi nuni a kansa, shine sallah a duk lokacin da mutum ya yi tsarki ya yi alwala, kuma shi yana daga cikn mafi kwaɗayin ayyuka kuma sababi na shiga aljanna.
  2. An so yin sallah bayan kowace alwala.
  3. Tambayar (mutum) wanda ake koyi da shi ko mai tarbiyya game da aikin almajirinsa; dan ya kwaɗaitar da shi akan tabbata a kansa idan ya kasance mai kyau ne, inba haka ba to sai ya hana shi.
  4. Shaidar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa Bilal - Allah Ya yarda da shi - da cewa shi yana daga cikin 'yan aljanna.
  5. Wannan tambayar a lokacin sallar Asuba ce, a cikin wannan akwai nuni cewa hakan ya faru ne a cikin mafarki daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafarkin Annabawa gaskiya ne.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية