1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka

عَنْ عَمْرِو بْنِ الحَارِثِ خَتَنِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخِي أُمِّ المؤمِنين جُوَيْرِيَةَ بِنْتِ الحَارِثِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُم، قَالَ:
مَا تَرَكَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ مَوْتِهِ دِرْهَمًا وَلاَ دِينَارًا وَلاَ عَبْدًا وَلاَ أَمَةً وَلاَ شَيْئًا، إِلَّا بَغْلَتَهُ البَيْضَاءَ، وَسِلاَحَهُ، وَأَرْضًا جَعَلَهَا صَدَقَةً.

Daga Amr Ibul Haris ɗan uwan mai dakin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ɗan uwar ummul muminina Juwairiyya Bintul Haris - Allah Ya yarda da su -, ya ce:
Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka.

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 2739

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rasu bai bar dirhamin na azirfaba ko zinari ba, ko bawan da ya mallaka ko baiwar da ya mallaka ko raƙumi ko wani abu na dukiyaba, sai kawai farar alfadararsa wacce yake hawanta, da wani filin da ya bar shi waƙafi a lokacin da yake da lafiya saboda matafiya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Annabawa ba'a gadarsu.
  2. Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bari bayan mutuwarsa.
  3. (Annabi) tsira da amincin su tabbata agare shi ya rasu amma bai bar wani abin da yake da kima ba, saboda kyautarsa da kuma ciyarwarsa da kuma kyautatawarsa.
  4. Karmani ya ce: Wakilin suna a cikin faɗinsa (kuma ya sanyata) mai komawa ne ga duka ukun wato alfadarar da makami da fili bawai zuwa filin kawai ba.
  5. Al-Khitn: Ɗan'uwar mata, al-Ukhtani kuma ta ɓangaren mace.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية