1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?

عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِأَفْضَلَ مِنْ دَرَجَةِ الصِّيَامِ وَالصَّلاَةِ وَالصَّدَقَةِ؟» قَالُوا: بَلَى، قَالَ: «صَلاَحُ ذَاتِ البَيْنِ، فَإِنَّ فَسَادَ ذَاتِ البَيْنِ هِيَ الحَالِقَةُ».

Daga Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?" Suka ce: Eh, ya ce: "Yin sulhu tsakanin waɗanda ke rigima, domin ɓacin tsakanin waɗanda ke rigima shine mai askewa".

Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shi Sunan Tirmizi - 2509

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin bana baku labarin abin da ya fi ladan nafilar azimi da sallah da sadaka ba? Suka ce: Eh.. Ya ce: Yin sulhu tsakaknin masu rigima inda rigima take gadar da rabuwa da kuma kadaita da ƙiyayya da juyawa juna baya tsakanin mutane, domin abin da yake haifuwa akan ɓata waɗanda ke rigima na ƙiyayya wacce ita ce ɗabi'ar da sha'aninta shine ta halakar ta tunɓuke Addini da duniya kamar yadda aska take tunɓuke gashi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta hanyar tambayar sahabbai da kuma sasu shauƙin sanin amsa.
  2. Ɗaibi ya ce: Kwaɗaitarwa a kan sulhunta masu rigima da nisantar ɓata su; domin yin sulhu sababi ne na yin riƙo da igiyar Allah da kuma rashin rabuwa tsakanin musulmai, ɓacin masu rigima rabuwa ne a cikin Addini duk wanda ya yi sulhu ya kuma ɗauke ɓacinta zai samu daraja sama da abin da mai azimi mai tsayuwar dare mai shagalta da keɓantuwar kansa yake samu.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية