1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sharrinku?

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَقَفَ عَلَى نَاسٍ جُلُوسٍ، فَقَالَ:
«أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِخَيْرِكُمْ مِنْ شَرِّكُمْ؟» قَالَ: فَسَكَتُوا، فَقَالَ ذَلِكَ ثَلاَثَ مَرَّاتٍ، فَقَالَ رَجُلٌ: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، أَخْبِرْنَا بِخَيْرِنَا مِنْ شَرِّنَا، قَالَ: «خَيْرُكُمْ مَنْ يُرْجَى خَيْرُهُ وَيُؤْمَنُ شَرُّهُ، وَشَرُّكُمْ مَنْ لاَ يُرْجَى خَيْرُهُ وَلاَ يُؤْمَنُ شَرُّهُ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya ga wasu mutane suna zaune sai ya ce:
"Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sharrinku?" Ya ce: Sai suka yi shiru, sai ya faɗi haka sau uku, sai wani mutum ya ce: Eh ya Manzon Allah, bamu labari da mafi alherinmu daga mafi sharrinmu, ya ce: "Mafi alherinku shine wanda ake fatan alherinsa kuma ake amincewa sharrinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba'a fatan alherinsa kuma ba'a amincewa sharrinsa".

Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi Sunan Tirmizi - 2263

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikin wasu mutane cikin sahabbansa suna zaune sai ya tambayesu, shin bana sanar daku in tunatar muku wanda yake shine mafi alherinku da wanda yake shine mafi sharrinku ba? Da ba su yi magana ba kuma basu amsa masa da komai ba, dan jin tsoron banbance alherinsu da sharrinsu, suka ji tsoron kunyata sai suka yi shiru. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake yi musu tambaya sau uku, sai wani mutum daga cikinsu ya amsa: Eh ya Manzon Allah, bamu labarin mafi alherinmu daga mafi sharrinmu. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana musu: Cewa mafi alherinku shine wanda ake sauraro kuma ake fatan (samun) alherinsa da kyautatawarsa da alherinsa, kuma ake amincewa sharrinsa dan haka ba'a jin tsoron ta'addancinsa da munanawarsa da kuma zalincinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba'a fata kuma ba'a sauraro ba'a kwaɗayin alherinsa da kyautatawarsa da alherinsa, kuma ba'a amincewa sharrinsa, kai ana jin tsoron ta'addancinsa da munanawarsa da kuma zalincinsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin mafi alherin mutane da mafi sharrinsu.
  2. Amfani da cuta masu kaiwa ga wani su ne mafi girma daga mai taƙaituwa.
  3. Kwaɗaitarwa akan kyawawan ɗabi'u, da kyakkyawar mu'amala tsakanin mutane, da gargaɗarwa daga zalinci da sharri da wuce gona da iri.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية