1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa ‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya

عَنْ هِشَامِ بْنِ حَكِيمِ بْنِ حِزَامٍ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّهُ مَرَّ عَلَى أُنَاسٍ مِنَ الْأَنْبَاطِ بِالشَّامِ، قَدْ أُقِيمُوا فِي الشَّمْسِ، فَقَالَ: مَا شَأْنُهُمْ؟ قَالُوا: حُبِسُوا فِي الْجِزْيَةِ، فَقَالَ هِشَامٌ: أَشْهَدُ لَسَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِنَّ اللهَ يُعَذِّبُ الَّذِينَ يُعَذِّبُونَ النَّاسَ فِي الدُّنْيَا».

Daga Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya wuce wasu mutane daga cikin manoma a Sham, haƙiƙa an tsaida su a cikin rana, sai ya ce: Meke damunsu? suka ce: Antsaresu ne saboda jizya, sai Hisham ya ce: Na shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
«‌Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2613

Bayani

Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - ya wuce wasu manoma daga baubayi a Sham, an tsayar da su a zafin rana, sai ya yi tambaya game da lamarinsu? Sai aka ba shi labarin cewa su an aikata musu haka ne saboda basu bada (jizya ba) alhali su suna da ikon hakan. Sai Hisham - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ina shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya akan zalinci ba tare da wani haƙƙi ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Jizya ita ce: Dukiyar da aka wajabtawa maza daga cikin ma'abota littafi (Yahudawa da Nasara) baligai mawadata maimakon kiyayesu da kuma zamansu a kasar Musulunci.
  2. Haramcin azabtar da mutane har kafirai ba tare da wani abinda yake wajabta hakan na shari'a ba.
  3. Gargaɗar da azzalumai daga zalinci.
  4. Riƙon sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ƙi.
  5. Nawawi ya ce: Wannan abin ɗauka ne akan azabtarwa ba tare da wani haƙƙi ba, dan haka azabtarwa da haƙƙi bata shiga cikinsa kamar ƙisasi, da haddi, da ta'azirai, da makanacin haka.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية