1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «قَالَ اللَّهُ: كَذَّبَنِي ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، وَشَتَمَنِي وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: لَنْ يُعِيدَنِي، كَمَا بَدَأَنِي، وَلَيْسَ أَوَّلُ الخَلْقِ بِأَهْوَنَ عَلَيَّ مِنْ إِعَادَتِهِ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا وَأَنَا الأَحَدُ الصَّمَدُ، لَمْ أَلِدْ وَلَمْ أُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لِي كُفْؤًا أَحَدٌ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Madaukakin sarki ya ce: ‘Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba. Amma karyatawar shi gare Ni shi ne fadinsa: (Allah) ba zai dawo dani ba (bayan mutuwa) kamar yadda Ya halicce ni a farko, ba wai halittar ta farkon ita ce mafi sauki gareNi daga dawowa da shi ba, amma aibantaNi shi ne fadinsa a kaina: Allah Yana da Da, alhali Ni Daya ne kwal wanda ake nufinSa da bukata Ban haifa ba, ba’a kuma haifeNi ba, kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Ni".

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 4974

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyanawa acikin Hadisi Kudsi cewa Allah - Mai girma da daukaka - Ya sanar game da mushrikai da kafirai cewa su suna karyataShi suna siffantaShi da tawaya da aibobi, kuma hakan bai kamacesu ba.
Amma karyatawar da suka yi wa Allah: Ita ce riyawarsu cewa Allah Ba zai dawo da su bayan mutuwarsu ba akaro na gaba, kamar yadda Ya haliccesu tun afarko da ba su, sai ya yi musu raddi da cewa Wanda Ya fari halitta daga babu mai iko ne akan dawo dasu kai hakan mafi sauki ne ma, duk da al'amarin dangane da Allah daidai ne halitta da dawowa, Allah Mai iko ne akan dukkan komai.
Amma aibantawar: To fadinsu: Cewa Shi Yana da Da, sai ya yi musu raddi da cewa Shi ne daya Kwal, Mai kadaituwa da dukkanin cika a sunayenSa da siffofinSa da ayyukanSa, abin tsarkakewa daga kowacce tawaya da aibi, abin nufi da bukata wanda baYa bukatuwa ga wani, kuma kowa mai bukatuwane gareShi, kuma bai zama mahaifi ga wani ba, kuma baShi da wani Da, kuma baShi da tamka, tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tabbatar da cikar iko ga Allah - Madaukakin sarki -.
  2. Tabbatar da tashi bayan mutuwa.
  3. Kafircin wanda ya musanta tashi bayan mutuwa ko ya danganta Da ga Allah - Madaukakin sarki -.
  4. Babu tamka ko kini ga Allah - Madaukakin sarki -.
  5. Yalwar hakurin Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da jinkirtawarSa ga kafirai watakila su zasu tuba su koma.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية