1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ:
سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «قَالَ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ مَا دَعَوْتَنِي وَرَجَوْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ عَلَى مَا كَانَ فِيكَ وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ لَوْ بَلَغَتْ ذُنُوبُكَ عَنَانَ السَّمَاءِ ثُمَّ اسْتَغْفَرْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ، وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ إِنَّكَ لَوْ أَتَيْتَنِي بِقُرَابِ الأَرْضِ خَطَايَا ثُمَّ لَقِيتَنِي لاَ تُشْرِكُ بِي شَيْئًا لأَتَيْتُكَ بِقُرَابِهَا مَغْفِرَةً».

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - ya ce:Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa. Ya kai ɗan Adam da zunubanka sun kai ƙololuwar sama, sannan ka nemi gafarata zan gafarta maka, babu ruwaNa. Ya kai ɗan Adam lallai cewa kai da ka zo min da kurakurai cikin ƙasa sannan ka gamu dani ba yi min tarayya da wani abu ba, da na zo maka da gafara cikinta".

Hasan ne Tirmizi ne ya ruwaito shi Sunan Tirmizi - 3540

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya faɗa a cikin hadisi Kudisi: Ya kai ɗan Adam muddin dai kana roƙoNa kana kwaɗayin rahamata, ba ka yanke ƙauna ba; zan suturta zunubanka zan shafesu batare da kulawa ba a cikinsu; koda wannan zunubin da sabon sun kasance daga manyan zunubai ne. Ya kai ɗan Adam ! Da zunubanka sun yawaita yawan da zasu cika abinda ke tsakanin sama da ƙasa ta inda suka kai sasanninta kuma suka game gefanta, sannan ka nemi gafarata; zan shafe zan gafarta maka dukkaninsu ba tare da kulawa da yawansu ba.
Ya kai ɗan Adam: Lallai kai da zaka zo min bayan mutuwa da zunubai da sabo cikin ƙasa, kuma ka zama mai tauhidi baka taranya wani abu daNi ba; dana fuskanci waɗannan zunuban da sabon da gafara cikin ƙasa; domin cewa Ni Mai yalwar gafar ne, kuma ina gafarta dukkan zunubai in banda shirka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Yalwar rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - da gafararSa da falalarSa.
  2. Falalar Tauhidi, kuma cewa Allah Yana gafarta zunubai da sabo ga masu Tauhidi.
  3. Haɗarin shirka kuma cewa Allah ba Ya gafara ga masu shirka.
  4. Ibnu Rajab ya ce: Haƙiƙa wannan Hadisin ya ƙunshi sabubba uku waɗanda gafarta zunubai suke samuwa da su: Na farko: Addu'a tare da ƙauna. Na biyu: Istgfari da neman tuba. Na uku: Mutuwa akan Tauhidi.
  5. Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alƙur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin alwala sabo da taba shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, (Mu’ujiza) da sauransu.
  6. Zunubai nau'i uku ne: Na farko: Shirka da Allah; wannan Allah ba Ya gafarta shi, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Lallai cewa shi wanda ya yi shirka da Allah to haƙiƙa Allah Ya haramta masa aljanna}. Na biyu: Zalintar bawa ga kansa a cikin abinda ke tsakaninsa da tsakanin Ubangijinsa na zunubai da sabo; domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - zai gafarta hakan, kuma zai ƙetare in Ya so. Na uku: Zunuban da Allah baYa barin komai daga garesu; su ne zalintar bayi sashinsu da sashi, babu makawa daga sakayya.

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو