1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi

عَنِ الزُّبَيْرِ بْنِ العَوَّامِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَأَنْ يَأْخُذَ أَحَدُكُمْ حَبْلَهُ، فَيَأْتِيَ بِحُزْمَةِ الحَطَبِ عَلَى ظَهْرِهِ، فَيَبِيعَهَا، فَيَكُفَّ اللَّهُ بِهَا وَجْهَهُ خَيْرٌ لَهُ مِنْ أَنْ يَسْأَلَ النَّاسَ أَعْطَوْهُ أَوْ مَنَعُوهُ».

Daga Zubair ɗan Awwam - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ɗayanku ya ɗauki igiyarsa, ya zo da curin itatuwa a gadan bayansa, ya saida su, Allah Ya kame fuskarsa da su, shi ne yafi alheri gare shi daga ya roƙi mutane sun ba shi ko sun hana shi».

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1471

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin mutane ya yi aiki kowane irin aiki ne koda zai ɗauki igiya ne, ya tattara itatuwa a gadan bayansa sai ya saida shi ya ci daga gare shi, ko ya yi sadaka da shi ya wadata daga mutane da shi kuma ya kare fuskarsa daga ƙasƙancin roƙo; shi ne ya fiye masa alheri daga ya tambayi mutane su ba shi ko su hanashi, roƙon mutane ƙasƙanci ne, mumini kuwa maɗaukaki ne ba ƙasƙantacce ba ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma tsarkaka daga gare shi.
  2. Kwaɗaitarwa akan aiki dan samun arziƙi, koda an jarrabi baligi da ƙaramar sana'a wulaƙantacciya a idanuwan mutane.
  3. Yaƙar da Musulunci yake yi wa roƙo; saboda haka ya wajabta yin aiki, ko da mai wahala ne; kamar saran ita ce misali.
  4. Roƙo ba ya halatta tare da iko akan aiki da kuma neman arziƙi.
  5. Roƙon sarki (shugaba) idan akwai buƙata ya halatta, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Haka kuma babu (laifi) a kan waɗanda idan sun zo maka don ka basu abin hawa sai ka ce: "Bani da abin hawan da zan baku," sai suka juya idanuwansu suna kwararar da hawaye don baƙin cikin ba su sami abinda zasu ciyar ba}. [Al-Taubah: 92].
  6. Wanda yake da larurar roƙo da kuma rauni akan neman kuɗi to ya halatta gare shi ya yi roƙo, amma kada ya yi naci, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Basa nacin roƙon mutane} [Al-Baƙara: 273].
  7. Nawawi ya ce: A cikinsa akwai: Kwaɗaitarwa akan sadaka, da kuma ci daga aikin hannunsa, da neman halal.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية