1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato

عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْلَ وَفَاتِهِ بِثَلَاثٍ يَقُولُ:
«لَا يَمُوتَنَّ أَحَدُكُمْ إِلَّا وَهُوَ يُحْسِنُ بِاللهِ الظَّنَّ».

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin wafatinsa da (kwana) uku yana cewa:
"Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2877

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da musulmi cewa kar ya mutu sai shi yana kyautatawa Allah zato da rinjayarwarsa ɓangaren ƙauna a lokacin mutuwa da cewa Allah Zai yi masa rahama kuma Zai yi masa rangwame, domin cewa tsoro abin nema ne dan kyautata aiki, wancan halin ba halin ayyuka ba ne, abin nema a cikinsu (shi ne) rinjayar ƙauna.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan shiryarwar al'ummarsa, da tsananin tausayinsa da ita a dukkan halayenta; har a cikin rashin lafiyar rasuwarsa yana yi wa al'ummarsa nasiha kuma yana shiryar da ita akan hanyoyin tsira.
  2. Al-Ɗaibi ya ce: Ku kyautata ayyukanku a yanzu har zatanku ga Allah ya kyautatu a lokacin mutuwa, domin cewa wanda ya munana aikinsa kafin mutuwa zatansa zai munana a lokacin mutuwa.
  3. Mafi cikar halaye ga bawa (shi ne) daidaituwar ƙauna da tsoro, da kuma rinjayar so; soyayya ita ce abar hawa, ƙauna kuma mai korowa ce, tsoro kuwa mai tuƙawa ne, Allah kuma Mai sadarwa ne da baiwarSa da kuma karamcinSa.
  4. Yana kamata ga wanda ya kasance makusanci daga wanda mutuwa ta halarto masa ya rinjayar da ɓangaren ƙauna da kyautatawa Allah zato, a cikin wannan hadisin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi haka kafin ya rasu da (kwana) uku.

Manufofin Fassarorin

50 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية