1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta

عَنْ أَبِي عُبَيْدٍ، مَوْلَى ابْنِ أَزْهَرَ، قَالَ:
شَهِدْتُ العِيدَ مَعَ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، فَقَالَ: هَذَانِ يَوْمَانِ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ صِيَامِهِمَا: يَوْمُ فِطْرِكُمْ مِنْ صِيَامِكُمْ، وَاليَوْمُ الآخَرُ تَأْكُلُونَ فِيهِ مِنْ نُسُكِكُمْ.

Daga Abu Ubaid, 'yantaccen Ibnu Azhar, ya ce:
Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1990

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani game da azimin ranar idin ƙaramar sallah da idin babbar sallah; amma idin ƙaramar sallah to ranar buɗa baki ce daga azimin watan Ramadan, amma ranar idin babbar sallah to ranar ci ce daga abubuwan layya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin azimin ranakun idin ƙaramar sallah da babba da kwanukan Tashriƙ; domin cewa su masu bi ne ga ranar babbar sallah sai dai ga wanda bai samu hadaya ba to azimin kwanukan tashriƙ ya halatta gare shi.
  2. Ibnu Hajar ya ce: An ce: Fa'idar siffanta ranaku biyun dan nuni ga illa a wajabcin cin abinci a cikinsu, shi ne rabewa daga azimi, da bayyanar cikarsa shi kaɗai da karya azimin abinda ke bayansa, ɗayan kuma saboda yanka wanda ake neman kusanci da yankansa dan a ci daga gare shi.
  3. An so ga mai huɗuba (liman) a cikin huɗubarsa ya tinatar da abinda yake rataye da lokacinsa na hukunce-hukunce kuma ya kintaci munasabobi.
  4. Halaccin ci daga abin yanka.

Manufofin Fassarorin

46 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية