1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar wadanda ke gabaninku

عَنْ أَبِي وَاقِدٍ اللَّيْثِيِّ رضي الله عنه:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمَّا خَرَجَ إِلَى حُنَيْنٍ مَرَّ بِشَجَرَةٍ لِلْمُشْرِكِينَ يُقَالُ لَهَا: ذَاتُ أَنْوَاطٍ يُعَلِّقُونَ عَلَيْهَا أَسْلِحَتَهُمْ، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، اجْعَلْ لَنَا ذَاتَ أَنْوَاطٍ كَمَا لَهُمْ ذَاتُ أَنْوَاطٍ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «سُبْحَانَ اللهِ! هَذَا كَمَا قَالَ قَوْمُ مُوسَى {اجْعَلْ لَنَا إِلَهًا كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ} [الأعراف: 138] وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ لَتَرْكَبُنَّ سُنَّةَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ».

Daga Abu Wakid Al-Laisi - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da ya fita zuwa Hunain ya wuce wata bishiya ta mushrikai ana ce mata: Ma'abociyar rataya, suna rataye makamansu akanta, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka sanya mana ma'abociyar rataya kamar yadda suke da ma'abociyar rataya, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki ya tabbata ga Allah! wannan kamar yadda mutanen Musa sukace ne: {Ka sanya mana wani ubangiji kamar yadda suke da iyayen giji} [Al-Aaraf: 138] Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar wadanda ke gabaninku".

Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 2180

Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa Hunain shi: Wani kwari ne tsakanin Makka da Da’if, Ya kasance a tare da shi akwai wasu daga sahabban da ba su dade da shiga Musulunci ba. sai suka wuce wata bishiya ana ce mata: "Ma'abociyar rataya", wato: Ma'abociyar rataye-rataye, mushirikai sun kasance suna girmamata kuma suna rataya makamansu akanta da wasunsu dan neman albarka (sa’a). sai suka nema daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanya musu wata bishiyar irinta, za su dinga rataya makamansu akanta, dan neman albarka (sa’a), Dan zatonsu cewa wannan al'amarin ya halatta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tasbihi dan inkarin wannan maganar, da kuma girmama Allah, kuma ya sanar da cewa wannan maganar ta yi kama da maganar mutanen (Annabi) Musa da suka ce da shi: {Ka sanya mana wani ubangiji kamar yadda suke da iyayen giji}, lokacin da suka ga wanda yake bautawa gumaka sai suka nemi ya zama suna da gumaka kamar yadda mushrikai suke da gumaka, kuma cewa wannan bin hanyar hanyarsu ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wannan al'ummar za ta bi hanyar Yahudawa da Nasara kuma za ta aikata irin aikinsu, dan gargadarwa akan hakan.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mutum yakan ga kyan abu yana zatan cewa zai kusantar da shi zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - alhali shi zai nisantar da shi daga Allah ne.
  2. Ya kamata ga musulmi ya tsarkake Allah ya yi kabbara idan ya ji abinda ba ya kamata a fada a Addini, da kuma lokacin mamaki.
  3. Yana daga shirka neman albarka daga bishiyoyi da duwatsu da wasunsu, ana neman albarka ne kawai daga Allah Shi kadai.
  4. Sababin bautar gumaka shi ne girmamasu, da lazimtuwa a gurinsu, da neman albarka da su.
  5. Wajabcin toshe kofofi da hanyoyin da za su kai zuwa ga shirka.
  6. Abinda ya zo daga nassosi a zargin Yahudawa da Nasara to gargadi ne garemu.
  7. Hani daga kamanceceniya da mutanen Jahiliyya da Yahudawa da Nasara, sai abinda dalili ya tabbatar akan shi yana daga Addininmu.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية