1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Sabuntawa Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da abinda aka saukar mana}

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ:
كَانَ أَهْلُ الْكِتَابِ يَقْرَؤُونَ التَّوْرَاةَ بِالْعِبْرَانِيَّةِ، وَيُفَسِّرُونَهَا بِالْعَرَبِيَّةِ لِأَهْلِ الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تُصَدِّقُوا أَهْلَ الْكِتَابِ وَلَا تُكَذِّبُوهُمْ، وَقُولُوا: {آمَنَّا بِاللهِ وَمَا أُنْزِلَ إِلَيْنَا} [البقرة: 136] الْآيَةَ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mazowa littafi sun kasance suna karanta Attaura da Ibirananci, kuma suna fassarata da larabci ga ma'abota Musulunci, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da abinda aka saukar mana} [Al-Baqara: 136] Aya".

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 4485

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar da al'ummarsa daga ruduwa da abunda mazowa littafi suke ruwaitowa daga littattafansu, Yayin da Yahudawa suka kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna karanta Attaura da harshen ibirananci, shi ne harshen Yahudawa, kuma suna fassarata da larabci, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, wannan a cikin abinda ba'a gane gaskiyarsa daga karyarsa; Wannan domin cewa Allah - Madaukakin sarki - Ya umarcemu mu yi imani da abinda aka saukar agaremu na Alkur’ani , da abinda aka saukar garesu na littafi, saidai cewa shi babu wata hanya garemu zuwa musan ingancin abinda suke hakaitowa daga wadancan littattafan da kuma mara kyansa, idan abinda zai bayyana gaskiyarsa daga karyarsa bai zo a shari'armu ba, Sai mu tsaya, Ba zamu gasgata su ba; dan kar mu zama abokanan tarayya tare dasu a cikin abinda suka canza shi, kuma kada mu karyatasu; watakila zai iya zama ingantacce, sai mu zama masu musun abinda aka umarcemu da mu yi imani da shi. Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni mu ce: {Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne}. [Al-Baqara: 136].

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Abinda mazowa littafi suka bada labarin shi ya rabu gida uku: Akwai bangaren da ya dace da Alkur’ani da sunna sai agasgatashi. Da bangaren da ya sabawa Alkur’ani da sunna to wannan batacce ne kuma za'a karyatashi. Da kashi na uku babu abinda yake nuni akan gaskiyarsa ko karyarsa a cikin Alkur’ani da sunna; to wannan za'a ruwaitoshi, ba za’a gasgatashi ko a karyatashi ba.

Manufofin Fassarorin

68 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
EL Ελληνικά اليونانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو