1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa

عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«حَقٌّ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ أَنْ يَغْتَسِلَ فِي كُلِّ سَبْعَةِ أَيَّامٍ يَوْمًا، يَغْسِلُ فِيهِ رَأْسَهُ وَجَسَدَهُ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 897

Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wajibi ne mai ƙarfi a kan kowanne musulmi baligi mai hankali ya yi wanka a kowanne kwana bakwai daga sati rana ɗaya, sai ya wanke kansa da jikinsa a wannan ranar; don neman tsarki da tsafta, mafi cancantar waɗannan kwanukan (ita ce) ranar Juma'a, kamar yadda aka fahimta daga sashin riwayoyi, wanka ranar Juma'a kafin sallah mustahabbi ne mai ƙarfi, ko da ya yi wanka ranar Alhamis misali, abinda ya cire shi daga wajabcin (shi ne) faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -: "Mutane sun kasance suna wa kawunansu hidima, sun kasance idan sun tafi zuwa Juma'a sai su tafi a yanayinsu: sai aka ce da su: Ina ma dai kun yi wanka". Bukhari ne ya ruwaito shi, a cikin wata riwayar ta shi: "A tare da su akwai wari" wato warin gumi da makamanncin hakan, a tare da hakan aka ce da su: Ina ma dai kun yi wanka

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Damuwa da kulawar musulunci game da tsafta da kuma tsarki.
  2. Wankan Juma'a mustahabbi ne mai ƙarfi don yin sallah.
  3. Ambaton kai ko da ambaton jiki ya tattaroshi; don ba shi muhimmanci ne.
  4. Wanka yana wajaba a kan duk wanda aka samu a tare da shi akwai wari abin ƙi wanda mutane suke cutuwa da shi.
  5. Mafi ƙarfin yini don yin wanka (shi ne) ranar Juma'a don falalarta

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية