عَنْ مَيْمُونَةُ أُمِّ المؤمِنينَ رضي الله عنها قَالتْ:
وَضَعْتُ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ غُسْلًا، فَسَتَرْتُهُ بِثَوْبٍ، وَصَبَّ عَلَى يَدَيْهِ، فَغَسَلَهُمَا، ثُمَّ صَبَّ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ، فَغَسَلَ فَرْجَهُ، فَضَرَبَ بِيَدِهِ الأَرْضَ، فَمَسَحَهَا، ثُمَّ غَسَلَهَا، فَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَذِرَاعَيْهِ، ثُمَّ صَبَّ عَلَى رَأْسِهِ وَأَفَاضَ عَلَى جَسَدِهِ، ثُمَّ تَنَحَّى، فَغَسَلَ قَدَمَيْهِ، فَنَاوَلْتُهُ ثَوْبًا فَلَمْ يَأْخُذْهُ، فَانْطَلَقَ وَهُوَ يَنْفُضُ يَدَيْهِ.

Daga Maimuna Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce :
Na ajiye wa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ruwan wanka, sai na kare shi da tufafi, sai ya saka a hannayensa, sai ya wankesu, sannan ya zuba da damansa akan hagunsa, sai ya wanke gabansa, sai ya goga hannunsa a kasa, sai ya shafe shi, sannan ya wanke shi, sai ya kuskure baki ya shaƙi ruwa, ya wanke fuskarsa da zira'in hannunsa biyu, sannan ya zuba a kansa sai ya kwaranyo ruwan akan jikinsa, sannan sai ya gusa kadan, sai ya wanke diga-digansa, sai na ba shi tufafi bai karɓa ba, sai ya tafi alhali yana kakkaɓe hannayensa.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 276

Bayani

Uwar muminai Nana Maimuna - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da siffar wankan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - na tsarki, lokacin da ta ajiye masa ruwa dan ya yi wanka da shi, kuma ta kare shi da labule, sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikata abinda ke tafe:
N farko: Ya zuba ruwa a hannayensa sai ya wanke su kafin ya shigar da su cikin abin wanka.
Na biyu: Ya zuba ruwa da hannunsa na dama akan hannunsa na hagu sai ya wanke gabansa; dan tsarkake shi daga abinda ya maƙale na alamar janaba.
Na uku: Ya bugi ƙasa da hannunsa sai ya shafe shi sannan ya wanke shi dan ya gusar da ƙazanta daga gare shi.
Na huɗu: Ya kurkure baki; ta hanyar shigar da ruwa a cikin bakinsa ya motsa shi ya kuma kurkure shi sannan ya zubar da shi, sai ya shaƙi ruwa; ta hanyar da ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da nunfashinsa, sannan ya fitar da shi dan ya tsarkake shi.
Na biyar: Ya wanke fuskarsa da zira'insa biyu.
Na shida: Ya zuba ruwa a kansa.
Na bakwai: Ya zuba ruwa a sauran jikinsa.
Na takwas: Ya juya daga gurinsa sai ya wanke diga-digansa a wani wurin daban ta inda bai wankesu ba kafin nan.
Sannan ta kawo masa wani mayafi dan ya tsane da shi, bai karɓa ba, sai ya fara shafe ruwan jikinsa da hannunsa yana karkaɗe shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Himmatuwar matan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - da siffanta mafi tsirfafan bayanan rayuwarsa; dan sanar da al'ummarsa.
  2. Wannan siffar wankan ɗaya ce daga cikin siffofin da suka tabbata daga annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - a cikin siffar cikakken wanka na janaba, amma siffa mai isarwa to ita ce ya game jikinsa da ruwa tare da kurkure baki da shaƙa ruwa.
  3. An halatta tsane jiki da mayani ko a bar shi bayan wanka ko alwala.

Manufofin Fassarorin

57 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية