1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati

عَنْ ‌عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنها أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ، ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَنْبَغِي إِلَّا لِعَبْدٍ مِنْ عِبَادِ اللهِ، وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ أَنَا هُوَ، فَمَنْ سَأَلَ لِيَ الْوَسِيلَةَ حَلَّتْ لَهُ الشَّفَاعَةُ».

Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 384

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nuna wa wanda ya ji mai kiran sallah da ya maimaita a bayansa, sai ya faɗi irin abinda ya fada, ban da Hai'ala biyu, cewa ya ce a bayansu: Babu dabara ba ƙarfi sai ga Allah. Sannan ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan gama kiran sallah, domin cewa wanda ya yi salati ɗaya a gare shi to Allah zai yi masa salati goma da shi, ma'anar salatin Allah ga bawanSa: shi ne YabonSa ga bawa a wurin Mala'iku.
Sannan ya yi umarni da a roƙa masa Allah Wasila - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ita ɗin wani matsayi ne a aljanna, shi ne mafi ƙololuwa, ba ta dace ba, kuma wannan matsayin ba zai samu ba sai ga wani bawa ɗaya daga dukkanin bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, ina ƙaunar in zama ni ne shi, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗa ne, don Tawalu’u; domin cewa idan shi wannan matsayin da yake babba ba zai kasance ba sai ga mutum ɗaya, to, ai wannan mutum ɗayan ba zai zama ba sai shi (Annabin) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin shi ne mafificin halitta.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa wanda ya roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila; to, cetonsa zai same shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa a kan amsawa mai kiran sallah.
  2. Falalar salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan amsawa mai kiran sallah
  3. Kwaɗaitarwa a kan roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila bayan salati a gareshi .
  4. Bayanin ma'anar Wasila, da ɗaukakar darajarta ta inda ba ta tabbata sai ga wani bawa ɗaya.
  5. Bayanin falalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da aka keɓanceshi da wancan babban matsayin.
  6. Wanda ya roƙi Allah Wasila ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - to, cetonsa zai ya halatta gare Shi.
  7. Bayanin ƙanƙar da kansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da ya nemi addu'a daga al'ummarsa na wannan matsayin, tare da cewa zai kasance gare shi.
  8. Yalwar falalar Allah da rahamarSa, aikin lada ɗaya (za a yi sakamako) da goma tamkarta.

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية