1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA

Sabuntawa Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ رَفَعَهُ:
فِي قَوْلِ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ: {وَمَنْ يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍ بِظُلْمٍ نُذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ} [الحج: 25] قَالَ: «لَوْ أَنَّ رَجُلًا هَمَّ فِيهِ بِإِلْحَادٍ وَهُوَ بِعَدَنِ أَبْيَنَ لَأَذَاقَهُ اللَّهُ عَذَابًا أَلِيمًا».

Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ruwaito shi Marfu'i:
A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".

Ingantacce ne Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi Al-Mustadrak Ala Al-Sahihain - 3461

Bayani

Abdullahi ɗan mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambata a cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Duk wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci to zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi}. [al-Hajj: 25], ya ce: Da ace wani daga cikin mutane zuciyarsa zata zantar masa cewa ya yi nufin aikata wani mummunan aiki a cikin Haramin Makka wanda zai halatta abinda Allah Ya haramta masa a cikinsa na haram da harshe ne ko kisa da gangan to cewa hakan zalinci ne, kuma da a ce ƙudirin niyyar a birnin Adan ne a cikin (kasar) Yaman to lallai shi mai cancantar Allah Ya azabtar da shi ne da azaba mai raɗaɗi saboda hakan, koda kuwa bai aikata shi ba, niyyar hakan kawai ta ishe shi .

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin matsayin da harami ya kebanta da shi da kuma girmama shi .
  2. Al-Sa'adi ya ce: A cikin wannan ayar mai girma, akwai wajabcin ganin alfarmar Harami, da tsananin girmama shi, da gargaɗarwa daga nufin yin saɓo a cikinsa da kuma aikata (saɓon).
  3. Al-Dahhak ya ce: Lallai mutum zai yi niyyar aikata kuskure a Makka alhali shi yana wata ƙasar daban sai arubuta masa (laifin) alhali bai aikata laifin ba.

Manufofin Fassarorin

35 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية