1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa

عَنْ سَعْدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
كُنْتُ أَرَى رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ، وَعَنْ يَسَارِهِ، حَتَّى أَرَى بَيَاضَ خَدِّهِ.

Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa.

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 582

Bayani

Sa'ad Ibnu Abi Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana ganin farin kundukukin (kumatun) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda tsananin waiwayensa idan zai sallame daga sallarsa a damansa a sallamar farko, haka a hagunsa a (sallama) ta biyu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin kai matuƙa a cikin waiwaye zuwa ɓangaren dama da kuma ɓangaren hagu.
  2. Halaccin sallama biyu zuwa dama da hagu.
  3. Nawawi ya ce: Da a ce zai yi sallama biyu a damarsa ko a hagunsa ko ta ɓangaren fuskarsa, ko ta farkon a hagunsa, ta biyun kuma a damansa sallarsa ta inganta kuma sallama biyun ta tabbata, sai dai ya rasa falala ta yadda ake yinsu .

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية