1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu

عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِنَّ الشَّيْطَانَ قَدْ أَيِسَ أَنْ يَعْبُدَهُ الْمُصَلُّونَ فِي جَزِيرَةِ الْعَرَبِ، وَلَكِنْ فِي التَّحْرِيشِ بَيْنَهُمْ».

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2812

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lallai Iblis ya yanke ƙaunar muminai masu sallah su dawo bautarsa da yi wa gunki sujjada a cikin tsibirin larabawa, sai dai cewa shi bai gusheba yana kwaɗayi, kuma bai gusheba ƙoƙarinsa da wahalarsa da tafiyarsa ba ta gushe ba a cusa rigingimu a zukatansu da gaba da yaƙe-yaƙe da fitintinu da makancin wannan a tsakaninsu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bautar Shaiɗan (ita ce ) bautar gunki; domin cewa shi ne mai umarni da ita kuma mai kira zuwa gareta, saboda dalilin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - game da (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi -: (Ya babana kada ka bautawa Shaiɗan...).
  2. Shaiɗan yana iya ƙoƙari a afkar da rigingimu da gaba da yaƙe-yaƙe da fitintinu tsakanin musulmai.
  3. Daga fa'idojin sallah a Musulunci cewa ita tana tsare soyayya tsakanin musulmai, kuma tana ƙarfafa alaƙar 'yan uwantaka tsakaninsu.
  4. Sallah ita ce mafi girman alamomin Addini bayan shaida biyu, saboda haka ne aka saki sunan musulmai (da) masu sallah.
  5. Tsibirin Larabawa yana da wasu keɓantattun abubuwa banda waninsa cikin garuruwa.
  6. Idan an ce haƙiƙa bautar gumaka ta faru a wasu daga sashin tsibirin Larabawa, alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: (Lallai Shaiɗan ya yanke ƙaunar cewa masu sallah su bauta masa...), to wannan labartawa ne game da abinda ya afku a cikin ran Shaiɗan na yanke ƙauna saboda abinda ya gani na nasarori, da shigar mutane a cikin Addinin Allah jama'a - jama'a, hadisin ya labarta ne game da zatan Shaiɗan da abinda yake sa ran zai afku, sannan waƙi'i (ya zama) saɓanin hakan dan wata hikimar da Allah - Mai girma da ɗaukaka - yake nufinta.

Manufofin Fassarorin

49 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية