1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace

عَن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا يَنْظُرُ الرَّجُلُ إِلَى عَوْرَةِ الرَّجُلِ، وَلَا الْمَرْأَةُ إِلَى عَوْرَةِ الْمَرْأَةِ، وَلَا يُفْضِي الرَّجُلُ إِلَى الرَّجُلِ فِي ثَوْبٍ وَاحِدٍ، وَلَا تُفْضِي الْمَرْأَةُ إِلَى الْمَرْأَةِ فِي الثَّوْبِ الْوَاحِدِ».

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 338

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana namiji ya kalli al'aurar namiji, ko mace ta kalli al'aurara mace.
Al'aura: Ita ce dukkanin abinda ake jin kunya daga gareshi idan ya bayyana, al'aurar namiji ita ce tsakanin cibiyarsa da gwiwoyinsa, mace dukkaninta al'aurace dangane da maza na nesa, (wadanda akwai aure a tsakanin su) dangane da mata kuwa ko maharramanta to ita zata bayyanar da abinda yake bayyana a al'adance a lokacin aikinta a cikin gida.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga kaɗaituwar namiji da namiji a tufafi ɗaya , ko ƙarƙashin mayafi ɗaya alhali suna cikin tsiraici, da kuma mace ta kaɗaita da mace a tufafi ɗaya ko ƙarƙashin mayafi ɗaya a tsiraice; Domin hakan zai iya kaiwa zuwa shafar al'aurar kowanne daga garesu, shafarta kuwa abin hanawa ne, kamar kallon al’amuran ne, kai shi ne ma mafi tsanani a hani; Saboda hakan zai iya kaiwa zuwa barna girma.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga kallon al'aurori in banda miji da matarsa.
  2. Kwaɗayin Musulunci akan tsarkake jama'a da rufe hanyoyi masu kaiwa ga alfasha.
  3. Halaccin duba al'aura idan buƙata ta kama ga hakan, kamar magani da makamancinsa akan ya kasance bada sha'awa ba.
  4. Musulmi an umarce shi ne da suturta al'aurarsa da rintse ganinsa daga al'aurar waninsa.
  5. An keɓanci hani da maza tare da maza da mata tare da mata; Domin ya fi ja ga duba da yaye al'aurori.

Manufofin Fassarorin

57 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية