1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira

عَنِ العَبَّاسِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، عَلِّمْنِي شَيْئًا أَسْأَلُهُ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ. قَالَ: «سَلِ اللَّهَ العَافِيَةَ»، فَمَكَثْتُ أَيَّامًا ثُمَّ جِئْتُ فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، عَلِّمْنِي شَيْئًا أَسْأَلُهُ اللَّهَ. فَقَالَ لِي: «يَا عَبَّاسُ، يَا عَمَّ رَسُولِ اللهِ، سَلِ اللَّهَ العَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ».

Daga Abbas ɗan AbdulMuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah, Allah - Mai girma da ɗaukaka -shi. Ya ce: "Ka roƙi Allah lafiya", sai na zauna wasu kwanuka sannan na zo sai na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah shi. Sai ya ce dani: "Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira".

Ingantacce ne ta wani bangaren Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 3514

Bayani

Baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya nema daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi addu'ar da zai roƙi Allah ita, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sanar da shi cewa ya roƙi Allah lafiya da kuɓuta daga illoli da aibuka a addini da duniya da lahira, Abbas ya ce: Bayan wasu kwanuka sai na dawo zuwa gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - karo na gaba ina tambayarsa ya sanar dani addu'ar da zan nemeta daga Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa yana mai nuna masa kauna: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roki Allah lafiya dan tunkude kowace cuta da jawo kowane alheri da anfani a duniya da lahira.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Maimaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ita kanta addu'ar ga Abbas lokacin da ya tambaye shi karo na biyu yana nuni akan cewa lafiya ita ce mafi alherin abinda bawa zai roƙi UbangijinSa.
  2. Bayanin falalar lafiya, kuma a cikinta akwai tattarowar alherin duniya da lahira.
  3. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan neman ƙari na ilimi da alheri.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية