عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
قَالَ لِي النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اقْرَأْ عَلَيَّ»، قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَأَقْرَأُ عَلَيْكَ، وَعَلَيْكَ أُنْزِلَ؟ قَالَ: «نَعَمْ» فَقَرَأْتُ سُورَةَ النِّسَاءِ حَتَّى أَتَيْتُ إِلَى هَذِهِ الآيَةِ: {فَكَيْفَ إِذَا جِئْنَا مِنْ كُلِّ أُمَّةٍ بِشَهِيدٍ، وَجِئْنَا بِكَ عَلَى هَؤُلاَءِ شَهِيدًا} [النساء: 41]، قَالَ: «حَسْبُكَ الآنَ» فَالْتَفَتُّ إِلَيْهِ، فَإِذَا عَيْنَاهُ تَذْرِفَانِ.

Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mini: «Ka yi mini karatu» Na ce: Ya Manzon Allah, shin na yi maka karatu, alhali kai aka saukarwa? Ya ce: «Eh» sai na karanta Surat al-Nisa'i har sai da na zo wannan ayar: {To yaya al'amarin zai kasance idan muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida kan waɗannan al'ummar?”. {al-Nisa'i 41]. ya ce: «Ya isa haka» sai na juya gurinsa, sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 5050

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya karanta masa wani abu na Alƙur'ani, sai ya ce; Ya Manzon Allah, ta yaya zan karanta maka alhali kai aka saukarwa?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni ina son in ji shi daga wanina, sai ya karanta masa Suratu al-Nisa'i yayin da ya kai ga faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki -:{To yaya al'amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida akan waɗannan al'ummar?} Wato yaya halinka da halin al'ummarka zasu kasance idan Muka zo da kai kana mai shaida ga al'ummarka cewa kai ka isar musu da saƙo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka tsaya da karatun a yanzu, Ibnu Mas'uda - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai na juya wajensa sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye dan tsoron mauƙifin (alƙiyama), da kuma tausayin al'ummarsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Nawawi ya ce: An so sauraren Alƙur'ani da karkata zuwa gare shi da kuka a wurin karatun, da kuma la’akari da ma'anoninsa, kuma an so neman karantawa daga waninsa dan ya saurare shi, kuma hakan ya fi kai matuƙa a fahimta da kuma la’akari da ma'anoni akan ya karanta da kansa.
  2. Akwai lada a cikin sauraren karatun Alƙur'ani kamar yadda yake akwai a cikin karanta shi.
  3. Falalar Abdullahi bin Mas'ud - Allah Ya yarda da shi -, inda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya so ya ji karatun daga bakinsa, wannan yana nuni akan kwaɗayin Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda ad shi - akan neman Alƙur'ani da haddace shi da kuma kyautata shi.
  4. Falalar yin kuka dan tsoron Allah - Mai girma da ɗaukaka - a lokacin jin ayoyinSa, tare da lazimtar nutsuwa, da kyakkyawan yin shuru, da kuma rashin kururuwa.

Manufofin Fassarorin

32 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية