1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma

عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ، فَرَدَّ عَلَيْهِ ثُمَّ جَلَسَ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَشْرٌ» ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ، فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ، فَقَالَ: «عِشْرُونَ» ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ، فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ، فَقَالَ: «ثَلَاثُونَ».

Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma» Sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Ashirin», sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Talatin».

Hasan ne Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Tirmizi da Ahmad da kuma Darimi Sunan Abi Dawud - 5195

Bayani

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata agare ku) sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: An rubuta masa lada goma, sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah, (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada ashirin, sannan wani ya zo sai ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada talatin; wato kowane lafazi yana da lada goma.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mai zuw shi zai fara wa waɗanda ke zaune sallama.
  2. Karin lada (yana kasancewa ne) da ƙarin lafazan sallama.
  3. Mafi cika a yin sallama: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma mafificiyar siga a amsa (sallama): Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Kuma aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa).
  4. Matakan sallama da amsawa masu wuce juna ne ladan ma haka.
  5. Koyawa mutane alheri da kuma faɗakar da su akan samun abinda ya fi.
  6. Ibnu Hajar ya ce: Da ace mai fara (sallama) zai ƙara (da rahamar Allah) an so a ƙara (da albarkarSa), da ace zai ƙara (da albarkarSa) shin a shara'anta ƙari a cikin amsawar? haka nan da ace mai fara (sallama) ya yi ƙari akan (da albarkarSa) shin an shara'anta masa hakan, (Imam) Malik ya fitar a cikin Muwaɗɗa daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Sallama tana ƙarewa ne zuwa albarka.

Manufofin Fassarorin

43 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية