1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba

عَنْ أبي سَعيدٍ الخُدريَّ رضي الله عنه قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم ِ:
«إزْرَةُ المُسْلمِ إلى نصفِ السَّاق، وَلَا حَرَجَ -أو لا جُنَاحَ- فيما بينَهُ وبينَ الكعبينِ، وما كان أسفلَ منَ الكعبين فهو في النار، مَن جرَّ إزارَهُ بطرًا لم يَنْظُرِ اللهُ إليه».

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".

Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad Sunan Abi Dawud - 4093

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mayafin (tufafin) namiji musulmi, shi ne dukkan abinda yake suturta rabin ƙwauri na ƙasa daga maza, halaye uku ne: Na farko: Abinda yake mustahabbi shi ne ya zama zuwa rabin ƙwauri. Na biyu: Wanda ya halatta ba tare da karhanci ba shi ne abinda ke ƙasansa (ƙwauri) zuwa idan sawu; sune ƙasusuwa biyu masu bayyana a mararrabar ƙwauri da diga-digi. Na uku: Wanda aka haramta shi ne ya zama ƙasa da idan sawu, kuma ana jiye masa tsoron kar wuta ta taɓa shi, idan kuma ya zama dan girman kai ne da nishaɗi da shisshigi to Allah ba zai yi duba zuwa gare shi ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wannan siffar da kuma narkon ya keɓanci maza ne kawai, amma mata to antogance su daga hakan; domin cewa su an umarce su da suturta dukkan jikinsu.
  2. Dukkan abinda ke suturta rabin ƙasa daga maza to ana ce masa mayafi; kamar wando, da tufa da waninsu, kuma shi ya shiga cikin hukunce-hukunce na shari'a abin ambata a cikin wannan hadisin.

Manufofin Fassarorin

44 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
YO Yorùbá Yoruba
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية