1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki

عَنْ مُعَاوِيَةَ الْقُشَيْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، مَا حَقُّ زَوْجَةِ أَحَدِنَا عَلَيْهِ؟، قَالَ: «أَنْ تُطْعِمَهَا إِذَا طَعِمْتَ، وَتَكْسُوَهَا إِذَا اكْتَسَيْتَ، أَوِ اكْتَسَبْتَ، وَلَا تَضْرِبِ الْوَجْهَ، وَلَا تُقَبِّحْ، وَلَا تَهْجُرْ إِلَّا فِي الْبَيْتِ»

Daga Mu'awiyya alKushairi - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki".

Hasan ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad Sunan Abi Dawud - 2142

Bayani

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - menene haƙƙin mata akan mijinta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wasu al'amura, daga cikinsu:
Na farko: Kada ka keɓanci kanka da abin ci banda ita; kai ka ciyar da ita a duk lokacin da ka ci abin ci.
Na biyu: Kada ka keɓanci kanka da tufatarwa da tufafi, kai ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), hak idan ka yi aiki kuma ka samu iko.
Na uku: Ba'a dukanta sai da wani sababi da buƙatuwa, idan ya buƙatu zuwa dukanta dan ladabtarwa ko dan barinta wasu farillai to sai ya zama duka ba mai sa rauni ba; kuma ba'a dukan fuska; domin cewa fuska ita ce mafi girman gaɓɓai kuma mafi bayyanarsu kuma ta ƙunshi wasu sasanni manya da gaɓɓai masu laushi.
Na huɗu: Kada ka yi zagi ko ka ce : Allah Ya munana fuskarki; kada ka danganta koda wani abu daga jikinta zuwa munin da shi ne kishiyar kyau; domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne wanda Ya suranta fuskar mutum da jikinsa, kuma Ya kyautata halittar kowane abu, zargin halitta yana komawa ne zuwa zargin Mahalicci tsarki ya tabbata ga Allah.
Na biyar: Kada ka ƙaurace sai a wurin kwanciya, kuma kada ka juya mata baya, kada ka juyar da ita zuwa wani gidan daban; wataƙila hakan a cikin abinda afkuwarsa yake sabawa ne daga ƙauracewa tsakanin miji da mata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗayin sahabbai akan sanin haƙƙoƙin da bada su ga masu su wajibi ne akansu, da kuma sanin haƙƙoƙin su.
  2. Wajabcin ciyarwa da tufatarwa da wurin zama ga mace akan mijinta.
  3. Hani daga munanawa na ma'ana da wanda ake gani.
  4. Daga munanawa wanda aka hana daga gare shi ya ce: Ke ƙabilarki ba ta da daraja, ko daga mummunan dangi kike, ko mai kama da hakan.

Manufofin Fassarorin

48 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية