1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«رَغِمَ أَنْفُ رَجُلٍ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ، وَرَغِمَ أَنْفُ رَجُلٍ دَخَلَ عَلَيْهِ رَمَضَانُ ثُمَّ انْسَلَخَ قَبْلَ أَنْ يُغْفَرَ لَهُ، وَرَغِمَ أَنْفُ رَجُلٍ أَدْرَكَ عِنْدَهُ أَبَوَاهُ الكِبَرَ فَلَمْ يُدْخِلاَهُ الجَنَّةَ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba".

Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 3545

Bayani

Mummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sindi ya ce: A taƙaice cewa kowane mutum daga waɗannan haƙiƙa ya samu abinda da badan kasawa daga gare shi ba da ya sami wani rabo mai yawa na alheri, yayin da ya kasa har hakan ya wuce shi to haƙiƙa ya taɓe kuma yayi hasara.
  2. Kwaɗaitarwa akan salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duk lokacin da aka ambaci sunansa.
  3. Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari da zage damtse ga ibada a cikin watan Ramadan.
  4. Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari a cikin biyayya ga mahaifa da kuma girmamasu, musamman ma a lokacin tsufa.

Manufofin Fassarorin

46 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية