1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace

عَنْ أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَطْعِمُوا الجَائِعَ، وَعُودُوا المَرِيضَ، وَفُكُّوا العَانِيَ».

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 5373

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi shi ne ya ciyar da mayunwaci, ya ziyarci mara lafiya, ya fanso wanda aka ribace.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan taimakekeniya tsakanin musulmai.
  2. Kwaɗaitarwa akan ciyar da mayunwaci mai buƙatar cin abinci, to wannan an yi umarni a ciyar da shi.
  3. Halaccin gaida mara lafiya; dan rage masa raɗaɗi, da yi masa addu'a, da samun lada, da wanin haka.
  4. Kwaɗaitarwa akan fansar wanda aka ribace idan kafirai sun ribace shi, hakan ko dai bada biyan wani abuba dan tsamo shi daga cikinsu, ko ta hanyar musayar fursuna kafiri daga cikin waɗanda aka ribato; wato: Ta hanyar musaya.

Manufofin Fassarorin

32 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية