1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba

عَنْ عَبْدَ اللهِ بْنِ عَمْرٍو رَضيَ اللهُ عَنْهُمَا يَقُولُ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ لَقِيَ اللهَ لَا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا لَمْ تَضُرَّهُ مَعَهُ خَطِيئَةٌ، وَمَنْ مَاتَ وَهُوَ يُشْرِكُ بِهِ لَمْ يَنْفَعْهُ مَعَهُ حَسَنَةٌ».

Daga Abdullahi Ibnu Amr Ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba"

Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi Musnad Ahmad - 6586

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya mutu kuma ya gamu da Allah yana mai kaɗaita Allah ba ya hada wani da abu da shi to shi yana daga cikin 'yan aljanna, ko da an yi masa uƙuba da zunubinsa a cikin wuta. Wanda ya mutu alhali yana hada wani abu da shi to wani kyakkyawan aiki ba zai yi amfani tare da shirkarsa ba; kuma aljanna haramun ce gare shi .

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gargaɗarwa daga shirka, kuma cewa ita ce mafi girman zunubai da kurakurai, kuma cewa Allah baYa gafarta ta.
  2. Falalar tauhidi, kuma shi Tauhidi yana wajabta shiga aljanna; ko da bayan an yi azaba ne.
  3. Muhimmancin tabbata akan tauhidi har zuwa mutuwa, da kuma rashin aikata kishiyarsa na shirka.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية